Jarman Kano Farfesa Isa Hashim, ya bayyana Shehu Abdullahi dan Fodiyo a matsayin masanin fannonin ilimi da dama. Farfesa Hashim ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da ta-hakikin littafin Shehu Abdullahi dan Fodio da aka fi kira da Abdullahi Gwandu, mai suna Kifayatu Du’afa’is Sudan, wanda Dokta Sani Musa Ayagi da Dokta Hamid Ibrahim suka yi aiki a kansa.
Bikin kaddamar da littafin da aka yi a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, domin nuna godiyarsa ga cika shekara 50 a karagar mulki, Farfesa Isa Hashim ya ce:
“Allah Ya kebance Shehu Abdullahi Gwandu da baiwa da falalar da mutane kadan ke samun irinta. Shi marubuci ne, mai wa’azi ne, kuma yana koyarwa ga jagoranci da aikin Jihadi da ya himmatu a kai.”
Jarman na Kano, ya bayyana littafin ‘Kifayatu Du’afa’is Sudan,’ a littafin tafsiri mai shafuka 120, a matsayin wanda ya tattaro fannonin ilimi daban-daban. Ya ce idan aka tattara tafsirinsa na Diya’ul Ta’awil Fi Ma’anit Tanzil da na Kifaya, to za su kai shafi dubu da 700.
Shi kuwa dan Majen Kano, Malam Sanusi Lamido Sanusi, wanda ya yi ta’aliki a kan wannan muhimmin littafin tafsiri da Shehu Abdullahin Gwandu ya rubuta, don raunanan masu ilimi, ya yaba wa manyan malaman addinin da suka yi hidima kan wannan aiki, sannan ya bayar da shawarwari kan yadda za a kara daga darajarsa.
“Shehu Abdullahi ya rairayo wannan littafi ne daga cikin babban littafinsa na tafsiri wato Diya’ut Ta’awil Fi Ma’anit Tanzil, wanda ya cika shi da fannonin ilimi masu yawa kamar ilimin kira’o’in Alkur’ani da maganganun malaman mazhabobin fikihu daban-daban da fannonin ilimin harshen Larabci na Nahwu da Balaga. Saboda ganin masu rauni wajen ilimi ba za su samu cikakken amfani da littafin Diya’ut Ta’awil ba, sai ya rairayo wannan littafi ya sanya masa suna Kifayatu Du’afa’is Sudan, wato Littafin Tafsiri Mai gamsarwa ga Masu Raunin Ilimi na Mutanen Biranen Sudan,” inji Malam Sanusi Lamido Sanusi.
Ya ce saboda matsayin ilimin Shehu Abdullahi Gwandu ne Shehu Usman dan Fodio yake ce a kansa a cikin littafinsa Najmul Ikwan, cewa: “Jama’a ku kula da rubuce-rubucen dan uwana Abdullahi saboda ya himmatu da kulawa da tsare zahirin Shari’a.”
Malam Lamido Sanusi ya ce daliban ilimi da dama da a yanzu suka zama manyan malamai sun taka matakan ilimi ne ta hanyar yin hidima ga littafan da Shehu Abdullahi ya rubuta.
Da Aminiya ta tuntubi Dokta Sani Musa Ayagi wanda ya yi ta-hakikin littafin, ya ce babu abin da zai ce illa godiya ga mahalarta taron, tare da fatan alheri ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawarsu, don samun nasarar aikin. “Wannan taro karama ce daga karamomin da Allah Ya yi wa Shehu Abdullahi. Kuma na himmatu wajen ganin a samar cibiyar nazarin ilimi da za ta ci gaba da bibiyar littattafan Shehu Abdullahi,” inji shi.
Abdullahin Gwandu ya kebanta da baiwa a fannonin ilimi – Jarman Kano
Jarman Kano Farfesa Isa Hashim, ya bayyana Shehu Abdullahi dan Fodiyo a matsayin masanin fannonin ilimi da dama. Farfesa Hashim ya bayyana haka ne a…