Sanata Abdullahi Adamu shi ne sabon zababben Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa.
Ya zama Shugaban jam’iyyar ne bayan an zabe shi babu hamayya a karshen Babban Taron APC na kasa da ya gudana a dandalin Eagle Square da ke Babban Birnin Tarayya Abuja a karshen makon da ya gabata.
- Kotu ta yi fatali da bukatar beli da Abba Kyari ya shigar
- Abin da ya sa na fice daga PDP —Abba Gida-gida
An dai sha rade-radin cewa sabon Shugaban shi ne wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake so ya jagoranci jam’iyyar, lamarin da ya sa tilas sauran ’yan takarar suka janye masa.
Ya karbi shugabancin APC ne daga Kwamitin Rikonta na Kasa, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, sama da shekara daya bayan rushe jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole.
Wane ne Abdullahi Adamu?
Sanata Abdullahi Adamu dai dan majalisa ne mai ci da ke wakiktar mazabar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattijai.
Ya kuma taba zama Gwamnan Jihar Nasarawa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007. Shi ne zababben Gwamnan Jihar na farko.
An haife shi a garin Keffi, kuma ya fara karatunsa na firamare a garin, kafin daga bisani ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Makurdi a Jihar Binuwai ta yanzu, daga shekarar 1960 zuwa 1962.
Daga nan sai ya wuce Makarantar Fasaha ta Gwamnati da ke Bukuru, sai kuma Kwalejin Fasaha ta Kaduna, inda ya samu shaidar Babbar Difloma.
A shekarar 1992, Sanata Abdullahi ya samu digirinsa a fannin Shari’a daga Jami’ar Jos, sannan ya samu shaidar zama lauya a shekarar 1993.
Ya fara shiga harkokin siyasa ne tun a 1977, inda aka zabe shi cikin ’yan majalisar da suka tsara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Jamhuriya ta Biyu.
Kazalika, yana daya daga cikin mambobin Kwamitin Tsara Kundin Tsarin Mulki zamanin mulkin marigayi Shugaban Kasa, Janar Sani Abacha, a shekarar 1994.
Ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a shekarar 1999 karkashin jam’iyyar PDP inda ya yi nasara, kuma an sake zabensa a wa’adi na biyu a shekarar 2003.
Kazalika, Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaba na farko na sabuwar Kungiyar Gwamnonin Najeriya daga 1999 zuwa 2004.
2023: Wadanne kalubale ne a gaban shi?
Kusan za a iya cewa bayan kammala Babban Taron, babban abin da ke gaban jam’iyyar a yanzu shi ne kakar zabukan 2023.
Sabbin shugabannin jam’iyyar dai su ne za su ja ragamarta har bayan zaben shekara ta 2023.
Zaben dai zai zama zakaran gwajin dafi wajen tantance ko har yanzu APC na da farin jinin da za ta sake lashe zaben na badi.
Babban kalubalen da ke gaban sabon shugabancin shi ne na ganin jam’iyyar ta fitar da ’yan takarar da za su lashe mata zabukan masu zuwa.
Sai dai masana da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa akwai babban aiki a gaban sabon shugaban, musamman wajen sake hada kan ’ya’yan jam’iyyar, musamman a Jihohin da ake fama da rikicin shugabanci.
Shin zai iya cire wa APC kitse a wuta?
Babbar tambayar da ke labban ’yan Najeriya ita ce ko sabon shugaban zai iya cire wa APC kitse a wuta, musamman wajen sake dinke sassan da ke rikici da juna a jihohi.
Mutane dai na ganin dadewa da gogewar da yake da ita a fagen siyasa za su taka muhimmiyar rawa wajen sake hada kan ’yan jam’iyyar.
Amma babban abin jira a gani shi ne ko zai kammala wa’adinsa lafiya ba tare da an rabu dutse hannun riga irin na baya.