Gwamnatin Kano ta sanar da shirinta na gina gidaje ga mutanen da suka rasa muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamna kan yaɗa labarai, Sunusi Bature ya fitar a wannan Alhamis.
- Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD
- NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024
A cikin sanarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, wannan tallafin gidajen zai taimaka matuƙa wajen rage raɗaɗin tasiri da ambaliyar ruwan ta haddasa tare da bai wa magidanta damar tsugunar da iyalansu wuri guda.
Gwamnan Abba ya ce, gwamnatinsa na aikin haɗin gwiwa da Ma’aikatar Jin-ƙai da Rage Raɗaɗin Talauci domin samar da abinci da wasu kayayyaki ga mutanen da lamarin ya shafa.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan yayin zaman Majalisar Zartarwas da ya jagoranta, ya kuma bayyana shirin gwamnatinsa na rarraba kashin farko na kujeru da tebura 200,000 ga ɗaliban makarantun sakandire da firamare domin inganta yanayin koyo da karantarwa.
Kazalika, gwamnan ya yaba da yanayin komawar ɗalibai makarantu bayan hutun zangon ƙarshe na 2023/2024 da ya ƙare a wannan makon.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta ayyukanta na yi wa makarantu kwaskwarima da gyare-gyaren da take aiwatarwa a halin yanzu.