✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya sanya dokar hana fita a Kano

Zanga-zangar matsin rayuwa da aka soma a fadin jihar ta rikiɗe zuwa tarzoma.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a fadin Jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar yau a Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin na zuwa ne bayan zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa da ta rikiɗe zuwa rikici.

Bayani sun tabbatar da cewa zanga-zangar matsin rayuwa da aka soma a fadin jihar ta rikiɗe zuwa tarzoma bayan wasu matasa sun fara afka wa wuraren ajiye abinci suna wawashewa.

Hakan ya haifar da arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

A cikin bayanin nasa, gwamnan na Kano ya ce: “A taron tsaro na gaggawa da muka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kano, gaba ɗayanmu mun yanke shawarar ƙaƙaba dokar hana fita ta awa 24 domin ganin an dawo da doka da oda.”

Ko a jiya Laraba gwamnan ya nemi masu zanga-zangar da su guji tashin hankali, har ma ya gayyace su zuwa gidan gwamnati domin kai ƙorafinsu.

“Ina tabbatar muku cewa gwamnati ba za ta lamunci irin waɗannan ayyukan ba,” in ji shi yayin da yake yi wa ƴan kasuwa da sarakunan gargajiya, da malaman addini jawabi a gidan gwamnati.

“Maimakon haka, ina miƙa goron gayyata ga masu son yin zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji daɗin sauraren koke-kokensu kuma mu gudanar da tattaunawa mai ma’ana.”