Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta ce dakataccen tsohon Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Abba Kyari bai tsere daga gidan yarin Kuje ba bayan harin da aka kai.
Abba Kyari, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume kan zargin safarar miyagun kwayoyi, an aike da shi gidan yarin na Kuje.
- Idan na zama Shugaban Kasa yajin aikin ASUU zai zama tarihi – Kwankwaso
- Limamin cocin da ya ce ya san ranar da Annabi Isah zai bayyana wakilin Shaidan ne – CAN
A baya dai ana ta nuna fargabar cewa watakila Abban ya tsere daga gidan bayan wasu maharan sun farmaki gidan tare da sakin daruruwan fursunoni.
Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindigar suka fada gidan sannan suka saki fursunonin, ciki har da wadanda ake zargi da kasancewa rikakkun ’yan Boko Haram.
Amma a karin bayanin da ya yi kan batun, kakakin NCoS na Najeriya, Umar Abubakar, ya ce Abba Kyari yana nan bai tsere ba.
Haka nan, ya ce “Fursunoni 879 ne suka tsere sakamakon harin. Sai dai ya zuwa hada wannan rahoton, an sake kama mutum 443 daga cikinsu, ana tsare da mutum 551 yanzu haka, yayin da har yanzu ana kan neman mutum 443 da suka tsere, hudu daga ciki sun rasa ransu kana mutum 16 sun ji rauni kuma ana ci gaba da yi musu magani.
Ya ci gaba da cewa, “Sashen tattara bayanai na hukumar (CIMS) tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Shaidar Dan Kansa (NIMC), za su yi aiki tare wajen bin diddigi da kuma kamo fusunonin da suka tsere.
“Ana tabbatar wa jama’a cewa DCP Abba Kyari da wasu muhimman mutanen da ake tsare da su a gidan yarin suna nan, ba su tsere ba.
“Idan za a iya tunawa, bayan harin da aka kai a Gidan Gyaran Hali na Agbolongo a Jihar Oyo, Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya gana da jagororin jami’an tsaron da ke karkashin kulawarsa wanda a sakamakon haka aka samar da Rundunar Tsaro ta Hadin Gwiwa wadda ta kunshi jami’an tsaro daban-daban da za yi aiki don hana ci gaba da kai hare-hare gidajen yarin kasar nan.
“Ya zuwa lokacin da aka kai harin gidan yarin Kuje, muna da sojoji 38 baya ga jami’an ‘yan sanda da na Sibul Difens da DSS da NSCDC da kuma namu jami’an da muke da su. Duka wannan, kokarin da Ministan ke yi ne wajen ci gaba da kare gidajen yarinmu.