✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida ya fara biyan ’yan fansho 5,000 hakkokinsu

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da biyan Naira biliyan biyar daga cikin bashin hakkokin ’yan fansho 5,000 da gwamnatinsa ta gada

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kaddamar da biyan Naira biliyan biyar daga cikin bashin hakkokin ’yan fansho 5,000 da gwamnatinsa ta gada a jihar.

Gwamna Abba ya ce mutum 5,000 da za a biya hakkokinsu sun hada da yan fanshon da suka rasu kafin a biya su kudaden fansho da garatuti daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Ya shaida wa taron fara biyan kudaden a ranar Asabar cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da biyan hakkokin yan fanshon da yawansu ya kai Naira biliyan 48.

Abba Gida-gida ya kuma bayyana cewa yankan albashin ma’aikatan jihar da ake yi ba bisa kaidaba da sunan bangarensu na kudin fansho, ya zama tarihi.

A jawabinsa, Kwamred Abdullahi Tsohon Garba, wanda ya wakilici Shugaban Kungiyar Yan Fansho ta Kasa (NUP) Kwamred Godwin Abumisi, ya ce abin yawa ne yadda gwamnan ke biyan hakkokin yan fansho a daidai lokacin da wasu takwarorinsa gwamnoni suka fi mayar da hankali kan wasu matsaloli a jihohinsu.

Ya bayyana cewa biyan hakkokin Naira biliyan biyar ya  nuna idan aka ci gaba, nan gaba za a gama biyan duk bashin hakkokin yan fansho a Jihar Kano.

A nasu jawaban, Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamred Amimu Abdulsalam da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafizu Abubakar sun shawarci yan fanshon da cewa kada su bari albashinsu da gwamnatin baya ta rika yankewa da sunan fansho ba bisa kaida ba ya tafi a banza.

Sun kuma shawarci ’yan fanshon da su kai kara ga hukumomin yaki da almundahana domin ganin an kwato musu hakkokinsu.