✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida ya ci gaba da rusau a Kano

An ci gaba da rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Kano ta ci gaba da aikin rusau a jihar inda aka wayi garin Lahadi ta kara rushe wasu gine-gine.

Daga cikin wuraren da gwamnatin jihar ta kara rusawa akwai gine-ginen da aka yi a jikin filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Bayan haka kuma gwamnatin ta rushe wasu shaguna da ke jikin makarantar sakandire ta Kofar Nasarawa.

Sa’annan gwamnatin ta rushe gine-ginen da ke jikin makarantun sakandire na Duka Wuya da ta Goron Dutse.

Kasa da mako guda bayan kama aiki Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya soma cika alkawarin da ya dauka na rusa duk wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba da kuma kwato duk wani wuri na gwamnati da aka sayar da aka yi gini ba bisa ka’ida ba.

Wannan lamari ya tayar da kura matuka a Kano da ma wasu jihohi inda wasu suke goyon bayan hakan wasu kuma suka nuna rashin amincewarsu.

Lamarin ya jawo musayar yawu tsakanin tsoffin gwamnonin jihar ta Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya nuna bacin ransa kan rusau din inda ya ce gwamnatinsa ta bi doka wurin duka ayyukan da ta yi inda har ya yi ikirarin cewa da ya hadu da Kwankwaso da sai ya sharara masa mari.

Sai dai Kwankwason wanda ya gana da Shugaba Tinubu ya ce ya shaida wa shugaban kasa duk abin da Gandujen ya yi a Kano kuma a cewar Kwankwason.

Haka kuma Shugaba Tinubun ya amince da a ci gaba da gudanar da rusau din a Kano.

Dangane da batun mari kuwa, Kwankwason ya ce su Ganduje duk yaransa ne a siyasa domin ba za su iya kallon fuskarsa ba ma.