Gabanin bikin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kadarorinsa ga hukumar da’ar ma’aikata ta jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
- Gwamna Buni ya yi wa fursunoni 115 afuwa
- Ganduje ya rantsar sabon Kwamishina ’yan sa’o’i kafin ya bar mulki
Abba Gida-Gida ya ce bayyana kadarorinsa nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin gwamnatinsa mai zuwa.
Sanarwar ta kara da cewa, “A yau, na cika hakkin da kundin tsarin mulki ya dora min na bayyana kadarorina kafin na shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayu.
“Aiki ne na hidimta wa al’umma; na shirya tsaf don yin wannan aiki.
“Bugu da kari za mu yi aiki don dawo da martabar Kano da kuma kawo ci gaba ga dukkanin ma’aikatu.”
Abba ya ba da tabbacin cewa dukkan jami’an gwamnati da suka hada da masu rike da mukaman siyasa da za su yi aiki a gwamnatinsa, za su bi tsarin bayyana kadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.