✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida ya ayyana lokacin tura ɗalibai kasashen waje karatu

Sarki Nasiru Ado ya ce ya kai ziyarar ce domin yi wa gwamnan Barka da Sallah.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce rukunin farko na ɗaliban da gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun digirinsu na biyu za su fara tafiya ketare a watan Satumba na wannan shekarar. 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun gwamnan, Hisham Habib ya fitar ranar Asabar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya kai masa ziyarar Barka da Sallah a Fadar Gwamnatin Kano.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na bai wa ilimi fifiko, inda ya ce daga hawansa kan mulki ya sake buɗe makarantu 20 da gwamnatin da ta gabata ta rufe, tare da sake bude makarantun koyar da harkokin addinin musulunci na kananan hukumomin 44 da ke domin samar da ingantaccen ilimi ga al’umma.

Gwamna Abba Kabir ya kuma gode wa Sarkin saboda wannan ziyarar, yana mai yabawa da da irin rawar da sarakunan gargajiya suke takawa wajen adana tarihi da al’ada da zaman lafiya da cigaba a Jihar Kano.

Da yake nasa jawabin, Sarki Nasiru Ado ya ce ya kai ziyarar ce domin yi wa gwamnan Barka da Sallah, sannan ya ba shi shawarar samar da takin zamani mai rahusa ga manoma don inganta harkokin noma a Kano.

Sarkin ya kuma bukaci gwamnatin da ta samar da tsarin wayar da kan mutane akan muhimmancin dasa bishiyoyi da samar da rijiyoyin burtsatse a yankunan karkara don inganta rayuwar al’ummar.

Kazalika, ya shawarci gwamnan kan bullo da dabarun da za su kwadaitar da masu zuba jari domin inganta tattalin arzikin Jihar Kano.