Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce a watan Maris Mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa.
- Sojoji sun ceto mutum 30 da aka sace a Nasarawa
- ‘Dalilin gaza inganta wutar lantarki daga zamanin Obasanjo zuwa Buhari’
Gano man a rijiyar Keana ta Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.
A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.”
Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin.
Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lalata muhalli.
“Dole a gaggauta fara aikin nan saboda komai yanzu na sauyawa a duniya. Nan da shekara 10 ba lallai ne kowa ya yarda ya zuba jarinsa a harkar man ba matukar ba ya san zai ci riba ba. Saboda haka idan muka fara da wuri, ina ganin zai fi,” in ji Mele Kyari.