✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A watan gobe za a fara gasar Firimiya ta Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce akwai yiwuwar a fasar gasar rukuni-rukuni na Najeriya a watan gobe, kamar yadda kafar watsa labaran wasanni…

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce akwai yiwuwar a fasar gasar rukuni-rukuni na Najeriya a watan gobe, kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Africanfootball.com ta kalato.
Hukumar ta ce ta yi haka ne don ba kungiyoyin kwallon kafar da za su fafata a gasar Zakarun Kulob-Kulob na Afirka (Champions League) da kuma wacce za ta fafata a gasar cin Kofin kalubale na Afirka (Confederation Cup) damar shiryawa sosai.
Kulob din Enyimba na Aba zai fafata a gasar Zakarun Kulob na Afirka yayin da Warri Wolbes kuma zai fafata a gasar cin Kofin kalubale na Afirka.
“Za mu fara gasar da wuri ne don mu ba kulob-kulob din da za su wakilci Najeriya a gasanni daban-daban da za a fara a watan Fabrairun 2016 damar shiryawa sosai”, inji daya daga cikin jami’an Hukumar NFF wanda bai so a ambaci sunansa.
A shekaranjiya Laraba ne  Hukumar NFF ta amince da watan Janairu a matsayin watan da za a fara gasar Firimiya a taron shekara-shekarar (AGM) da ta yi a Abuja.