Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi masu ruwa da tsaki na duniya baki daya da su tabbatar an wadatar da kowace kasa a fadin duniya da rigakafin cutar Coronavirus da aka samar a kwanan nan.
Shugaba Buhari ya yi wannan kira ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba.
- ‘Ina da kwarin gwiwar mace za ta iya gadon Buhari a mulkin Najeriya’
- Yadda kungiyar IPOB ta kashe Musulmai da sunan #EndSARS —Okonkwo
Bayan bayyana farin cikinsa a kan rigakafin cutar Coronavirus wadda kamfanin Pfizer ya samar mai tasirin kashi 90 cikin 100, Shugaba Buhari ya nemi a rarraba rigakafin a dukkanin kasashen duniya domin tsare lafiyar al’umma.
“Na yi murna da rahoton samuwar rigakafin cutar coronavirus mai tasirin kashi 90 cikin 100, don wannan babban ci gaba ne ga duniya.”
“Dole ne duniya ta tabbatar an rarraba tare da wadatar da dukkan kasashen duniya da rigakafin domin tsare lafiyar mutane,” inji Buhari.
A ranar Litinin ne kamfanin hada magunguna na kasar Amurka, Pfizer, da kuma na BioTech, suka sanar cewa gwajin baya bayan nan na rigakafin cutar Coronavirus da suka kirkiro, ya nuna yana da ingancin sama da kashi 90 cikin 100, wanda hakan ya zarce abin da aka zata a baya.
Shugaban kamfanin Pfizer, Albery Bourla ne ya shelanta hakan a ranar Litinin dangane da matakin gwaji na uku da aka yi a kan rigakafin.