A Takaice…
Asamaoh Gyang ne zai jagoranci Ghana a gasar cin kofin duniya
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Ghana Kweshi Appiah ya bayyana cewa ya yanke shawarar shahararren dan kwallon kungiyar kwallon kafar Ghana Asamaoh Gyang ne zai zama Kyaftin a gasar cin kofin duniya da zai gudana a kasar Brazil a watan Yuni mai zuwa.
Gyang da yanzu haka yake buga wa kungiyar kwallon kafa ta Al Ain da ke Hadaddiyar Daular Larabawa an fara rade-radin zai koma kulob din West Ham United da ke Ingila ne a wannan wata na Janairu idan an bude kakar saye da sayar da ’yan kwallo.
Gyang ya zuwa kwallaye 39 daga cikin wasanni 76 da ya yi wa kasar Ghana kuma ya taimaki Ghana kai wa mataki na uku a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a bara.
Ghana dai ta kai matakin kusa da na karshe (Semi-Final) ne a gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu a shekarar 2010 bayan kasar Uruguay ta fitar da ita a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A gasar cin kofin duniya mai zuwa Ghana za ta fafata ne a rukunin G tare da kasashen Jamus da Amurka da kuma Fotugal.
Kulob din Chelsea ya yi asarar Naira biliyan 11
Kulob din Chelsea da ke Ingila ya bayar sanarwar yin asarar Fam miliyan 49.4 kwatankwacin Naira biliyan 11 da miliyan 515 a kakar wasan da ta wuce.
Sai dai duk da haka kulob din ya ce bai saba kai’dar gudanar da harkar kasuwanci a karkashin dokar Hukumar shirya wasan kwallo ta Nahiyar Turai (UEFA Financial Fair Play Regulations) ba.
Robin ban Persie ya kusa warkewa -Moyes
dan wasan gaban kulob din Manchester United da ke Ingila Robin ban Persie ya kusa murmurewa daga raunin da ya samu a makwannin baya.
Kocin kulob din Dabid Moyes ya ce a halin yanzu dan kwallon ya fara yin atisaye kuma ana sa ran zai fara buga wasa nan da ’yan kwanaki masu zuwa.
ban Persie, mai kimanin shekara 30, shi ne dan kwallon da ya fi zura kwallo a raga a kulob din Manchester a shekarar bara amma ya zuwa wannan lokaci bai yi wa kulob din wasanni biyar da suka wuce ba saboda rauni.