Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi
A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan ya zura kwallonsa ta tara a raga a gasar rukunin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
Real Madrid ta doke kulob din FC Copenhagen ne da ci biyu babu ko daya a wasan, kuma Ronaldo ne ya zura kwallo ta biyu a raga.
Wannan kwallo ta sa Ronaldo ya zarce tarihin da dan kwallon Italiya Inzaghi ya kafa a kakar wasa ta shekarar 2002 zuwa 2003 da kuma wacce Herman Crespo ya kafa a kulob din Inter Milan a shekarar 2002 zuwa 2003 da wacce Ruud ban Nistelroy na kulob din Manchester United ya yi a shekarar 2004 zuwa 2005 da kuma ta Zlatan Ibrahimobic na kulob din PSG a kakar wasa ta bana, inda dukkansu suka zura kwallaye takwas-takwas a zagayen farko na gasar.
Don haka a yanzu Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan ya zuwa kwallo tara a raga a zagayen farko a gasar.
Frank Ribery ne Gwarzon dan kwallon Faransa
An zabi shahararren dan kwallon Faransa da ke kulob din Bayern Munich da ke Jamus a matsayin Gwarzon dan kwallon Faransa a karo na uku, kamar yadda wata mujalla a Faransa ta ruwaito.
Ribery, dan kimanin shekara 30, a kakar wasan da ta wuce ne ya samu nasarar lashe manyan kofuna uku da suka hada da gasar rukunin Bundesliga ta Jamus da kofin kalubale da kuma kofin zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA Cahmpions League.
Ya samu nasara ne a zaben da Hukumar shirya kwallo ta Faransa ta yi bayan ya kada abokan takararsa Blaise Matuidi dan kwallon PSG da ke Faransa da kuma Paul Pogba da ke buga wasa a kulob din Jubentus da ke Italiya.
A shekarar 2007 da kuma 2008 ce Ribery ya lashe wannan kyauta sai kuma a bana a karo na uku. A halin yanzu ya fara kokarin kamo tsohon dan kwallon Faransa Thierry Henry da ya lashe kyautar har sau biyar.