✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…13

Nasri zai shafe wata biyu yana jinya dan kwallon gaba a kulob din Manchester City da ke Ingila Samir Nasri ya samu matsala a gwiwarsa…

Nasri zai shafe wata biyu yana jinya

dan kwallon gaba a kulob din Manchester City da ke Ingila Samir Nasri ya samu matsala a gwiwarsa a wasan da kulob din sa ya yi da na Newcastle United a gasar Premier a makon jiya da hakan ta sa zai shafe makwanni takwas yana jinya ba tare da buga kwallo ba.
dan kwallon ya samu matsala ne a arangamar da suka yi da dan kwallon Newcastle mai suna Mapon Yanga-Mbiwa.
Tuni Nasri ya aika sakon fatan alheri ga masoyansa a kafar sadarwarsa ta Twitter da Facebook inda ya nemi su yi masa addu’ar samun sauki don ganin ya koma harkar kwallo nan ba da dadewa ba.

 

Za a fara gasar rukuni ta kasa a ranar 23 ga watan gobe

Kwamitin shirya gasar rukuni-rukuni na kasa ajin kwararru da ke karkashin Hukumar NFF watau (League Management  Committee)  a ranar Litinin da ta gabata ne ya bayar da sanarwar za a fara gasar ta bana a ranar 23 zuwa 25 ga watan Fabrairu mai zuwa. Ita gasar kamfanin sadarwa na GLo ne yake daukar nauyinta.
Shugaban kwamitin lura da yadda gasar ke gudana Mista Nduka Irahor ne ya bayyana haka a Abuja jim kadan bayan kammala taro a tsakanin kwamitin da kuma shugabannin kungiyoyin kwallon kafa 20 da za su fafata a gasar.
A jadawalin gasar da kwamitin ya sanar an nuna kulob din Enyimba da ke Aba wanda ya zo na biyu  a kakar wasan da ta wuce zai fara wasansa na farko ne da kulob din Bayelsa United.
An samu tsaikon fara gasar ce har zuwa wannan lokaci saboda wadansu matsaloli da kwamitin ya rika tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwallon kafar da za su fafata a gasar don a cimma matsaya.
Mista Irahor ya ce a ranar 24 zuwa 25 ga wannan wata da muke ciki ne za a yi gasar zakaran gwajin dafi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa hudu da ake wa lakabi da Super Four da hakan zai share fagen shiga kakar wasa ta bana.

 

Seedorf ya zama kocin AC Milan

Clarence Seedorf, haifaffen kasar Holan da yake kwallo a kulob din AC Milan da ke Italiya ya daina buga kwallo don ya cigaba da horar da kulob din.
A ranar Talatar da ta wuce ne dan kwallon ya tabbatar da wannan labari bayan   kulob din ya yi masa tayin zama koci sakamakon sallamar tsohon koci Massimiliano Allegri saboda rashin tabuka abin a zo a gani a kakar wasa ta bana.
Kulob din AC Milan wanda ya lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) har sau bakwai ya sallami kocinsa ne jim kadan bayan kulob din Sassuolo ya lallasa na Milan da ci 3 da 4 a gasar rukukun Seri’a A na Italiya a ranar Asabar da ta wuce.
Seedorf, mai kimanin shekara 37, shi ne dan kwallon farko da ya lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) sau uku da kungiyoyin kwallon kafa daban-daban.  Ya taba lashe kofin da kulob din Ajad da ke Holland da na Real Madrid da ke Sifen da kuma AC Milan da ke Italiya.