✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 12

An zabi golan Najeriya wanda ya fi iya tsaron gida a Nahiyar Turai Golan Najeriya bincent Enyeama da yanzu haka yake buga kwallo a kulob…

An zabi golan Najeriya wanda ya fi iya tsaron gida a Nahiyar Turai

Golan Najeriya bincent Enyeama da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Lille OSC da ke Faransa ne aka zaba a matsayin Gwarzon Golan da ya fi kowane kwazo a daukacin Nahiyar Turai a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014.
Kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta supersuport.com ta gudanar da wani bincike, an nuna bincent Enyeama ne ya fi kowane gola hana kwallo shiga raga idan aka kwatanta shi da wadansu gololi da ke yankin Turai a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014 da ke gudana a halin yanzu.
dan kimanin shekara 31, Enyeama an zura masa kwallaye takwas ne kacal daga cikin wasanni 19 da ya yi wa kulob din Lille OSC ya zuwa wannan lokaci.  Kuma ya lashe gwarzon dan kwallo a gasar rukuni-rukuni ta Faransa da aka fi sani da Likue 1 sau biyu a jere da hakan ta sa ya zarce  zaratan ’yan kwallo irin su Thiago Silba da Edison Cabani da Mathiue Balbuena da Radamel Falcao da kuma Zlatan Ibrahimobic da ke fafatawa a gasar.

 

Babu dan kwallon da Manchester United za ta saya a wannan wata -Moyes

Kocin kulob din Manchester United da ke Ingila  Dabid Moyes ya bayar da tabbacin babu wani dan kwallo da kulob din zai cefano a wannan wata na Janairu duk da an bude kakar saye da sayar da ’yan kwallo a yankin Turai.
Kocin ya ce dalilinsa na rashin neman sayo wani dan kwallo a wannan lokaci shi ne da wuya ya samu irin dan kwallon da yake bukata a wannan lokaci don abu ne mai wuya kulob da dama su saki zaratan ’yan kwallonsu a tsakiyar kakar wasa.
Ya zuwa yanzu kulob din Manchester United shi ne na bakwai a jerin kungiyoyin kwallon kafar da ke fafatawa a gasar rukunin Premier ta Ingila.
Kulob din Manchester dai yana tangal-tangal a kakar wasa ta bana inda ya zuwa yanzu ya rasa kofuna biyu daga cikin hudu da yake zawarci.
A ranar Lahadin da ta wuce kulob din Swansea City na Ingila ya yi waje da na United a gasar cin kofin kalubale na Ingila watau (FA Cup) da ci 2-1 sannan a ranar Talatar da ta wuce kuma kulob din Sunderland na Ingila ya yi waje da na United a kofin Capital One da ake fi sani da Carling Cup da ci 2-1 da hakan ta sa magoya bayan kulob din da dama suka yi hasashen da wuya kulob din ya tsinana abin kirki a kakar wasa ta bana.
Sai dai wani rahoto da kafar sadarwa ta Goal.com ta kalato ya nuna masu kulob din na Manchester United da ake wa lakabi da Glazer Family sun sha alwashin farfado da martabar kulob din inda suke tunanin ware wa koci Dabid Moyes Fam miliyan 200 kwatankwacin Naira biliyan 47 don cefano zaratan ’yan kwallo a tsakanin watanni 18 masu zuwa.