Mesut Ozil ya ji rauni
dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila Mesut Ozil ya ji ciwo a wasan da kulob dinsa ya yi da na Bayern Munich na Jamus a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a ranar Talatar da ta wuce. An tashi wasan ne da ci 1-1 sai dai duk da haka kulob din Arsenal ya fice daga gasar idan aka hada wasannin biyu inda Munich ta yi nasara da ci 3-1.
A hutun rabin lokaci ne Tomas Rosicky ya canja Ozil bayan dan kwallon ya samu rauni a jijiyoyin da ke karkashin cinyarsa da aka fi sani da hamstring a Turance.
Tuni koci Arsene Wenger ya tabbatar da raunin Ozil sai ya zuwa shekaranjiya Laraba ya ce bai san takaimaman kwanakin da Ozil shafe ba tare da buga kwallo ba har sai Likitoci sun gama yi masa gwaji.
“Tabataccen abu dai shi ne Ozil ba zai buga wasanmu da kulob din Tottenham a gasar rukunin Premier na Ingila a jibi Lahadi ba”, inji Wenger.
Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Sukotlan
Najeriya Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da kasar Sukotlan (Scotland) a ranar 28 ga Mayu mai zuwa. Za a yi wasan ne a filin wasa na kulob din Fulham da ke Ingila wanda ake wa lakabi da Craben Cottage Ground.
Ajent din Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) mai suna Jairo Pachon of Eurodata da ya dauki alhakin shirya wasan ne ya sanarda haka ga sashen wasanni na gidan Rediyon BBC a wata tattaunawa da aka yi da shi.
Ya ce wasan zai ba kocin Najeriya da ’yan kwallo da kuma magoya baya damar ganin yadda kasashen biyu za su barje gumi, kuma zai taimaki kocin da ’yan kwallon a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a watan Yuni mai zuwa.
Sannan ana sa ran kwanaki biyar bayan wasan, Najeriya za ta sake haduwa da Girka (Greece) a wasan sada zumunta a Amurka.