✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika yi wa shugabanni addu’a – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya nemi mutanen kasar nan su rika yi wa shugabanninsu na siyasa da addini addu’a domin su…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya nemi mutanen kasar nan su rika yi wa shugabanninsu na siyasa da addini addu’a domin su samu sauki da kwarin gwiwar daukar nauyin da Ubangiji Ya dora masu na jagoranci.

Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a ranar Asabar da ta gabata a wurin rabon Zakka da Wakafi na gundumar Goronyo a karamar Hukumar Goronyon da ke Jihar Sakkwato.

“dorewar addu’a ga shugabanni a koyaushe shi ne makamin samun nasarar jagorancinsu, shugabanni ba su bukatar komai a wajen talakawansu kamar yi masu addu’a da bayar da shawarwari mai kyau da za su taimaki al’umma don haka nake rokon ’yan Najeriya su dage ga yi wa jagororinsu addu’a ta samu nasarar sauke nauyin da aka aza musu. Shugabanni an dora musu nauyin kawo ci gaba a kasa da dora jama’a a turbar da ta dace wanda hakan ba ya samuwa sai da addu’a,” inji Sarkin Musulmi. 

Sarkin Musulmin ya jinjina wa Hukumar Zakkah da Wakafi musamman shugabanninta kan jajircewar da suka yi wajen taimakon mabukata da gajiyayyu da fatan za su dore da aikin.  Ya nemi mawadata a jihar su rika fitar da zakkarsu ta hannun hukumar da gwamnati ta kafa maimakon tara mutane ana ba su kudin cefanen rana daya. Kuma ya yi tir da wadanda suka mayar da bara a titi sana’a maimakon su nemi sana’ar da za su yi su taimaki kansu.

Shugaban Hukumar Malam Lawal Maidoki ya yaba wa gundumomin Zakkah da Wakafi kan kokari da tsayuwar dakarsu wajen karbo Zakkah da Wakafi daga hannun mutane. Sai ya bukaci iyayen kasa su kara tashi tsaye ga wannan aikin na Allah don samun lada mai yawa a gobe kiyama.

Ya ce za su zagaye gundumomi 86 na Jihar Sakkwato don karba da raba Zakka da Wakafi kuma aikin yana samun nasara fiye da bara, inda aka raba buhun gero kasa da 100 a bana kuma aka raba fiye da 200, kuma dabbobi ma sun ninka, haka kudin wakafi.