Majalisar Malamai ta jihar Gombe ta buƙaci mahukunta da su kula da tubabbun ’yan kalare kamar yadda ake kula da tubabbun mayakan Boko Haram.
Shugaban Majalisar, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a shelkwatar rundunar ’yan sanda da ke Gombe.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 7 ’yan gida ɗaya a Abuja
- ’Yan ta’adda sun yi wa matar aure yankan rago a Yobe
Sheikh Hamza wanda kuma shi ne shugaban kungiyar izala na Jihar Gombe, na wannan kira ne bayan ya kammala jawabin jan hankalin ’yan kalare fiye da matasa 100 da suka ajiye makamai suka tuba.
Malamin wanda ya yi jawabin a gaban Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman, ya ce ya kamata a kula da tubabbun ’yan kalarem kamar yadda ake kula da tubabbun ’yan Boko Haram wajen sauya musu tunani kuma a koya musu sana’a.
Ya yaba wa Kwamishinan ’yan sandan na bullo da wannan tsari domin samar wa Jihar Gombe dawwamammen zaman lafiya na ladabtar da matasan ta hanyar lalama har suka yarda suka ajiye makamai suka tuba.
Malamin ya kuma kirayi gwamnati da ta shigo ciki domin dafa wa kokarin Kwamishinan ’yan sandan wajen kara masa kwarin guiwar ci gaba da gudanar da irin wannan kokari.
Ya ce hakan zai inganta wanzuwar zaman lafiya a jihar kamar yadda a yanzu sace-sace da ta’addanci ya ragu sosai.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’yan sandan Hayatu Usman, ya ce ya bullo da wannan tsari ne domin ganin matasan sun zama nagari masu amfanar al’umma kamar kowa ba a kyale su suna tada hankali da gararamba da makamai suna cin zarafin mutane ba.
CP Hayatu Usman, ya kara da cewa ya yi magana da masu ruwa da tsaki da shugabnin al’ummomi wajen ganin cewa sun shigo sun bada ta su gudumawar wajen koya musu sana’oi da tallafa musu da jari don kar su yi tuban muzuru.
“Cikin mutum 100 koda guda 10 ne suka zo suka ce sun tuba kuma tuba na gaskiya ai an samu karuwa balle mutum sama da 100 suka ce sun ajiye sun hakura, hakan ba karamar nasara muka samu ba,” inji Kwamishinan.
Wasu daga cikin tubabbun ’yan kalaren da suka yi jawabai sun ce da yawansu rashin sana’a ne ya sa suka shiga harkar Kalare domin tare mutane su kwace musu kayayyakin su dan su samu yadda za su tafiyar da rayuwarsu.
“Mun yi tuba na gaskiya ne ba tuban muzuru ba kuma muddin gwamnati za ta taimake mu kamar yadda ta ce to kuwa sauran ma da ba su tuba ba za mu jawo su su ajiye makamai,” a cewarsu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa wadannan dai su ne kashi na biyu da suka ajiye makamai cikin makonni uku, inda a karon farko aka samu mutum 50 kuma har yanzu ana sa ran wasu za su sake tuba.