✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun yi wa matar aure yankan rago a Yobe

uni dai wannan lamari na kisan Malama Ammi Adamu ya zama maudu’in tattaunawa lunguna da sako na Yobe.

Ana fargabar cewa ’yan ta’adda sun kashe wata matar aure mai suna Ammi Adamu Mamman a gidan mijinta da ke rukunin gidajen Bra-Bra na Karamar Hukumar Damaturun Jihar Yobe.

Bayanai sun ce maharan sun kashe matar mai shekaru 42 ta hanyar yankar rago.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.

DSP Dungus ya ce hukumar binciken manyan laifuka ta jihar ta fara gudanar da bincike domin zakulo masu hannu a wannan aika-aika.

A cewar Dungus, mijin matar Abubakar Musa mai shekaru 43 da haihuwa, yana ci gaba amsa tambayoyi a hannun jami’an ’yan sanda.

Ya kara da cewa, “Bincike ya nuna cewa ma’auratan ma’aikata ne Jami’ar Jihar Yobe (YSU) Damaturu ne.

“Rundunar ta jajanta wa iyalan matar da ta rasu yayin da ake kokarin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.”

A halin da ake ciki, Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Yobe ta yi kakkausar suka kan aukuwar wannan mummunan lamari, inda ta yi kira ga hukumomin tsaro da su zurfafa bincike domin zakulo wadanda suka aikata wannan laifin.

“Muna kuma kira ga mambobinmu ’yan jarida da su bi diddigin lamarin ta hanyar ba da haɗin kai domin kama wadanda ake zargi da kuma hana afkuwar lamarin nan gaba,” in ji Shugaban NUJ na jihar, Kwamared Rajab Mohammed Ismail.

Tuni dai wannan lamari na kisan Malama Ammi Adamu ya zama maudu’in tattaunawa yayin da yake ci gaba da gudana a kan harsunan jama’ar Damaturu da ma Jihar ta Yobe baki ɗaya.