✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe mutum 6 a harin gidan rawa a Yobe

Wannan shi ne hari na biyu da ‘yan ta’addan suka kai gidan rawar, yayin da a shekarar 2022 ’yan sun kai hari a wani gidan…

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ISWAP ne sun kashe mutum shida a wani harin gidan rawa da suka kai unguwar Kwari da ke Karamar Hukumar Geidam a Jihar Yobe.

Bayanai sun ce ’yan ta’addan sun kai hari gidan rawar ne a yayin da mahalartansa ke shakatawa da daddare, inda suka buɗe musu wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin garin na Geidam da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewar ’yan ta’addan sun kai farmaki ne da misalin karfe 2 na tsakar daren Alhamis wayewar garin Juma’ar.

Ya bayyana cewa faruwar lamarin ne ya sa mazauna garin suka tsere domin tsira da rayukansu, la’akari da harbe-harben da ’yan ta’addan suka riƙa yi babu kakkautawa.

Wasu majiyoyi sun tabbatar wa wakilinmu cewa kawo yanzu an gano gawarwaki shida yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.

“An gano gawarwaki shida, sun kuma kona mota daya da wasu gidaje da ba a san adadin su ba,” kamar yadda majiyar ta bayyana.

“Wannan dai shi ne hari na biyu da ‘yan ta’addan suka kai gidan rawar, yayin da a shekarar 2022 ’yan ta’addan sun kai hari a wani gidan mata masu zaman kansu da ke unguwar ta Kwari, inda suka kashe mutane 10 ciki har da mata.”

Da Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ASP Abdulkarin Dungus kan batun, ya ce kawo yanzu lamarin na hannun sojojin da suka fara kai dauki domin tunkarar ’yan ta’addan.