✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata masu zanga-zanga sun kona gidan basaraken Bokkos a Filato

Hare-haren da aka kai a jijiberin Kirsimeti sun shafi kauyuka 23 inda aka kashe mutum kusan dari biyu.

Wasu mata masu zanga-zanga sun cinna wuta a gidan Michal Monday Adanchi, hakimin garin Bokkos da ke Karamar Hukumar Bokkos a Jihar Filato.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na wannan Juma’ar.

Majiyar ta ce an gudanar da zanga-zangar ce bayan hukumomi sun kama wasu mazauna yankin da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai a wasu kauyukan Bokkos a lokacin Kirsimeti.

Bayanai sun ce matan sun fara bayyana fushinsu ne a ofishin ’yan sanda dangane da kamen da aka yi wa  ‘yan garin Bokkos.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga bisani ne kuma matan suka nufi fadar basaraken da suke zarginsa da hannu a kamen domin nuna rashin dadinsu.

Ana tsakar haka ne matan masu zanga-zanga suka cinna wa fadar basaraken wuta kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, wanda wakilinmu ya tuntuba, ya ce zai yi karin haske a kan lamarin da zarar sun kammala tattara bayanai.

A jiya Alhamis ce dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kama mutum takwas da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi a ranar jajibiren Kirsimeti.

Hare-haren dai sun shafi kauyuka 23 inda aka kashe mutum kusan dari biyu.