✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kula da iyalan Marigayi Audu Bako

Edita na karanta Zinariya a Aminiya ta ranar Juma’a 4 ga watan Satumba, inda Hajiya Zainab Audu Bako ta yi bayanin rashin tallafa wa iyalan…

Edita na karanta Zinariya a Aminiya ta ranar Juma’a 4 ga watan Satumba, inda Hajiya Zainab Audu Bako ta yi bayanin rashin tallafa wa iyalan marigayi Alhaji Audu Bako. Hakika ban ji dadi ba. Kowa ya san irin kyawawan ayyukan da Marigayi Alhaji Audu Bako ya yi a Jihar Kano da Najeriya.
Dubban ma’aikata da ’yan kwnagila da ’yan kasuwa sun samu arziki a lokacin da yake gwamna a Jihar Kano. Wasu da yawa muna ganinsu da kamfanoni da gidaje, amma ba su kula da abin da marigayin ya bari ba.
Duk da haka zan jinjina wa tsohon gwamna, yanzu kuma Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da ya bai wa Hajiya Zainab Audu Bako mukamai har biyu. Shi ma ya yi ayyuka masu kyau a Kano, amma sai ga shi ana so a yi masa bita-da-kulli. Aiu duk wanda ya yi aiki kan gaskiya da adalci a kasar nan ba a cika yaba masa ba.
Hajiya Zainab da ’yan uwanki ku yi hakuri, amma duk wani aiki da ake yi a Jihar Kano, a kan ayyukan Marigayi Gwamna Audu Bako ake yi.
Dubi madatsar ruwa ta Bagauda da Tiga da watari da dambatta da suaransu, duk shi ne ya yi. Ba don ya yi amfani da tunani ba, ba mu san yadda jihohi Kano da Jigawa za su kasance ba. Allah Ya jikansa, ya gafarta masa. Amin.
Daga M. Sule Musa Dutse, Musafas Publicity Agency. P. O. Bod 51 Dutse, Jihar Jigawa.