✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A koma gona don ita ce tushen arziki —Buhari

Buhari ya ce mafitar kasar ita ce kawai a koma gona a dirfafi noma haikan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a koma gona a rungumi harkar noma ka-in-da-na-in domin samun habakar tattalin arziki a kasar.

Cikin wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabiji na Channels a ranar Laraba da dare, Buhari ya ce mafitar kasar nan daga matsalar tattalin arziki ita ce kawai a koma gona a dirfafi noma haikan.

Duk da cewa bai yi na’am ba da kididdigar da matambayansa suka bijiro da ita ba wadda take nuna koma bayan da tattalin arzikin kasar ya samu a karkashin jagorancinsa, Buhari ya dage an kan cewa matsalar dai ita ce kurum a koma gona.

Buhari ya sake yin kira ga ’yan Najeriya da “su rika cin abincin da suke nomawa sannan su kuma noma abin da za su rika ci.”

Ya buga misali da cewa a halin yanzu a Najeriya ake noma shinkafar da ake ci, har ma ana fitar da ita ketare.