✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggautar dawo da wutar Arewa —Sanatoci

Sanatocin Arewacin Nijeriya sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta gyara wutar lantarkin yankin da ya lalace.

Sanatocin Arewacin Nijeriya sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta gyara wutar lantarkin yankin da ya lalace.

Kungiyar sanatocin yankin sun jaddada bukatar a hanzarta gyara layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Kaduna, wanda lalacewarsa ta jefa yankin cikin duhu na tsawon sama da mako guda.

Sanarwar da suka fitar dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Yar’adua bayan wani zama da suka yi a Kaduna ta kuma bukaci gwamnati ta tabbata ta dauki duk matakan da suka dace domin hana maimaituwar matsalar ko lalatawa ko sace kayan wutar lantarki.

Sanatocin sun yi wannan kira ne a ranar Asabar, a yayin da yankin rashin wutar ta durkusar da harkokin tattalin arziki da sauran al’amuran yau da kullum na iyalai da sauransu a yankin na Arewa.

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya sanar cewa ’yan ta’adda ne suka lalata layin lantakarin na Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ke samar da wuta ga yankin Arewa.

Kamfanin ya bayyana cewa, ya riga ya tanadi duk kayan da suka kamata domin gyara wutar, amma  ofishin mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro ya gargadi kamfanin game da hadarin shiga wurin, saboda gudun fadawa hannun ’yan bindiga.

Amma kamfanin ya bayyana cewa yana aiki tare da ofishin domin ganin cewa an gyara wutar nan ba da jimawa ba.