✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggauta hukunta wadanda ke da hannu a harin Mangu —Lalong

Dubban jama’a da suka hada da maza da mata da yara da tsofaffi na gudun hijira a Filato.

Gwamnatin Jihar Filato ta bukaci hukumomin da ke da hurumin kamo wadanda ke da hannu kan kashe-kashen da aka yi a Karamar Hukumar Mangu da kewaye, su bayyana wadanda suka kama don hukuntasu.

Gwamna Simon Lalong wanda ya yi wannan kira a wani taro da shugabannin jami’an tsaro a jihar, don sake duba matakan tsaro a Karamar Hukumar Mangu, ya ce, sun fahinci cewa akwai wadanda aka cafke da zargin hannu a rikicin.

Gwamnan ya kuma yi alkwarin tallafa wa dubban jama’a dake gudun hijira.

Bayanai sun ce matasa da mata daga sassa daban-daban na Jihar Filato sun taru a wuri guda don nuna alhininsu kan kashe-kashen da kuma bayyana bukatar gwamnati ta kawo karshen hare-haren da ake kaiwa kan jama’a.

Muryar Amurka ta ruwaito Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Karamar Hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono yana neman a samar musu da tsaro.

Shi ma Kansila mai wakiltar Mangu Ward one, Kabiru Iliyasu ya yi kira wa zababbun ‘yan majalisu su duba batun tsaro da idon basira.

Mutane fiye da dari ne bayanai ke nuna sun hallaka a hare-hare da aka kai a Karamar Hukumar Mangu cikin ‘yan kwanakin nan.

Kazalika, dabbobi da dama sun salwanta da gidaje masu tarin yawa da wuraren ibada da aka kona.

A halin yanzu dai dubban jama’a da suka hada da maza da mata da yara da tsofaffi ke gudun hijira wadanda kuma ke bukatar agajin gaggawa.