✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DAGA LARABA: Yadda Rashin Sanin Kimar Waliyyai Ke Shafar Auratayya

Yadda rashin daukar walittaka da muhimmanci ke kawo tabarbarewar zamantakewar aure

More Podcasts

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Matsalar rashin zaman lafiya da tausayin juna tsakanin ma’aurata a wannan zamani na daga cikin abubuwan da ke ci wa jama’a da dama tuwo a kwarya, lura da yadda matsalolin suke zama sanadin yawan mace-macen aure.

Baya ga matsalolin da ke samo asali daga ma’aurata da abokan huldarsu, shirin Daga Laraba ya gano yadda yin sakaci da walittaka ke zama sanadin tsamin dangantaka tsakanin ma’aurata, har ta kai ga mutuwar aure a wannan zamani.