Majalisar Wakilai ta buƙaci mahukunta da su gaggauta ceto ɗaliban nazarin likitanci 20 da aka sace a Jihar Benuwe.
Majalisar ta yi wannan kiran ne ga Babban Sufeton ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto ɗaliban masu karatun aikin likita da aka sace a yankin Arewa maso Tsakiyar Nijeriya.
- ’Yan bindiga sun saki bidiyon hakimin da suka sace a Sakkwato
- ’Yan sanda sun kama masu ƙwace waya 35 a Kaduna
Mai magana da yawun majalisar wakilan, Akin Rotimi Jr. ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Rotimi ya ce majalisar tana tare da Kungiyar Likitoci ta Nijeriya da Kungiyar Dalibai ta kasar, wajen neman jami’an tsaron sun yi duk abin da ya wajaba wajen ceto daliban lami lafiya.
Sanarwar ta ambato shugaban kwamitin kula da harkokin lafiya na majalisar, Dennis Idahosa, yana cewa, “Lafiyar dalibanmu na likitanci na da muhimmanci sosai.
“Kuma wannan lamari ba hari ba ne a kan wadannan matasan kwararru ba ne kadai, hari ne a kan makomar tsarinmu na kula da lafiya.”
Ya kara da cewa, “ba za mu sake mu kara rasa karin wasu rayuka ba saboda matsalar tsaro da take addabar kasarmu ba.
“Ba wani dalibi da zai kasance yana fargabar gudanar da harkokinsa da doka kasar nan ta yarda da su ba.
“Saboda haka muna bukatar matakan gaggawa na ba-sani-ba-sabo daga hukumomin tsaronmu wajen dawo da wadannan ɗalibai gida lafiya,” in ji Idahosa.
Majalisar ta ce tana ci gaba da goyon bayan duk wani mataki da za a ɗauka da zai inganta tsaro da lafiyar duk ’yan Najeriya, kuma za ta ci gaba da sa ido kan lamarin sosai.
Aminiya ta ruwaito cewa, ɗalibai 12 na Jami’ar Maiduguri ta Jihar Borno da takwas na Jami’ar Jos ta Jihar Filato ne suka faɗa komar masu garkuwa da mutanen a Jihar Benuwe.
Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe ta tabbatar da sace ɗaliban a ranar Alhamis, 15 ga watan Agustan nan tana mai cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu.
Lamarin ya rutsa da ɗaliban da ke kan hanyarsu ta halartar taron Ƙungiyar Ɗaliban Likitanci na shekara-shekara da za a gudanar a Jihar Enugu.
Arewacin Nijeriyar dai ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin samun kuɗin fansa, musamman ta hanyar tare tituna da kuma kai wa kauyuka farmaki daga lokaci zuwa lokaci.