✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A dauke jakala! A dauke jakala!

Wani Gwari ne direban tifa yana zuwa daukar yashi a wani kauye. To sai ya rika mugun gudu mutanen kauyen na ja masa kunne amma…

Wani Gwari ne direban tifa yana zuwa daukar yashi a wani kauye. To sai ya rika mugun gudu mutanen kauyen na ja masa kunne amma ya ki bari. Wata rana sai tsautsayi ya take zakarar wata tsohuwa, samarin gari kuwa suka tsare suka yi masa duka. Bayan kwana biyu sai ya taho a tifarsa sai ya hango bakar leda a kan hanya, sai ya taka birki yana cewa: “A dauke jakala! A dauke jakala!” Wato a dauke zakara. Sai da yaron motarsa ya sauko ya dauke ledar nan sannan ya wuce.
Daga MDG Abdullahi, Legas
08084624899