✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kashe ’yan Najeriya amma Tinubu ya fi damuwa da Zaɓen 2027 — SDP

Jam’iyyar SDP ta koka da cewa ’yan Najeriya suna rayuwa cikin fargici saboda rashin tsaro, amma gwamnati da ’yan siyasa sun fi mayar da hankalinsu…

Jam’iyyar adawa ta SDP buƙaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin siyasa a Najeriya su dai shagala da batun zaɓen 2027, su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara mayar da ƙasar tamkar filin kisa.

SDP ta bayyana cewa kashe-kashe ɗaruruwan mutane da ke faruwa a faɗin ƙasar nan – Arewa da Kudu – musamman a makonnin da suka gabata, na da matuƙar tayar da hankali.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na SDP, Araba Rufus Aiyenigba, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a, cewa abubuwan takaicin sun hada da da kisan mafarautan Jihar Kano a jihar Delta, baya ga ayyukan ’yan ta’adda da hare-haren da a ka yi wa mutane sama da 100 a sassan jihar Filato.

Ya ce gwamnatin da ke kan mulki a yau ta rasa duk wata dabara mai ma’ana kuma ta kasa samar da wata mafita da za ta dakatar da wannan zubar da jini da ke gudana, yayin da ƙasar nan ke saurin zama filin kisa.

“A wasu makonnin da suka gabata, an kai munanan hare-hare da kisan gilla da ƙona wasu maharba daga Jihar Kano a yankin Edo, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa arewa daga wani farauta a yankin Neja Delta.

“Haka kuma, a makon da ya gabata, an kashe sama da mutane ɗari ta hanyar kisan gilla tare da ƙona gidaje da yawa a Filato!

“An kuma ruwaito cewa wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna ‘Makmuda’ ta kashe mutane da yawa, wanda ya ƙara dagula al’amuran ƙasarmu,” in ji Aiyenigba.

Ya yi zargin cewa jami’an tsaron ƙasar nan suna ƙara kasala da rashin ƙarfi, yayin da gwamnatin da ke kan mulki ta rasa duk wata dabara mai ma’ana kuma ta kasa samar da wata mafita.

Ya ce, “Abin damuwa ne yadda duk waɗannan kashe-kashe da ɓarna ke faruwa ba tare da an yi wani abu ba.

“’Yan siyasa a bayyane yake cewa, sun fi damuwa ne kawai da batun zaɓen 2027 da ke tafe. Muna buƙatar yin aiki don tabbatar da tsaron masu zaɓe kuma mu mallaki ƙasa kafin ma a fara maganar zaɓe,” in ji shi.

Kakakin jam’iyyar SDP na ƙasa ya ce yanzu ne lokacin da Tinubu zai nuna ƙarfin hali da ƙarfin zuciya a matsayinsa na shugaba, ya kuma yi abin da ya dace don tabbatar da tsaron al’ummar Najeriya.

“A matsayinsa na shugaban ƙasa, wajibi ne ya tabbatar da tsaron ’yan ƙasa, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada, cewa jin daɗin jama’a da tsaro su ne babban manufar gwamnati.”

Ya ci gaba da mika ta’aziyyar jam’iyyar bisa rashe-rashen da aka yi a sakamakon wadannan matsalolin tsaro.