Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Jihar Kebbi kuma tsohon limamin sojoji, Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya shawarci gwamnatocin qasar nan su riqa tura mutane masu tsoron Allah da tsare gaskiya a matsayin jagororin maniyyata aikin Hajji a Qasa Mai tsarki.
Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Bunza da ke Jihar Kebbi, inda ya ce babbar matsalar da ke hana gudanar da aikin Hajji cikin nasara duk shekara daga Najeriya ita ce, gwamnatoci ba su nada jami’an alhazai nagari sai dai kwashi-kwaraf da suke da uwa a gindin murhu. “Saboda haka akwai buqatar gwamnatoci su riqa zabar mutane masu jin tsoron Allah da tausayi a matsayin jami’an alhazai, ta haka sai a riqa samun nasarar yin aikin Hajji a Najeriya,” inji shi.
Ya nuna takaicinsa a kan yadda jami’an alhazzai a Najeriya suke yin watsi da alhazai a Qasa Mai tsarki ba tare da nuna tausayawa ba wajen sauke nauyin da aka dora musu na kula da su. Ya shawarci gwamnatocin qasar nan su riqa cire siyasa wajen nada jami’an alhazai maimakon haka su riqa nada mutane masu gaskiya da riqon amana domin samun nasarar aikin Hajjin.