Gwamnan Katsina Aminu Masari ya bukaci sojoji da su tsananta yi wa ’yan bindiga luguden wuta ba tare da tsoron ko hakan zai ritsa da mutanen da babu ruwansu ba.
Masari ya ce matakan da sojoji suka dauka a kan ’yan bindiga sun takura miyagun ta yadda suke kokarin shigowa cikin al’ummomi, amma duk da haka kada sojoji su raga musu.
- An haramta nuna fina-finan garkuwa da mutane a Kano
- ‘Yadda mijina ke lakada min duka saboda ba na koshi’
Sai dai kuma ya shawarci sojojin da su dauki matakan takaita yiwuwar kashe mutanen da babu ruwansu idan irin hakan ta faru.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ziyarce shi domin sanin hakikanin nasarar da ake samu a yaki da ’yan bindiga.
A nasa bangaren, Lai Mohamme ya ce, “Sulhu da ’yan bindiga abu ne da gwamnati mai ci ba za ta lamunta ba.”
Shi ma da yake nasa jawabi, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, ya ce kuskure ne a yi sulhu da irin wadannan mutane.
“’Yan bindiga ba mutane ne masu addini ba, saboda haka a hada karfi sannan a dauki duk matakan da suka dace domin murkushe su,” inji basaraken.
– Matakin da aka dauka na samun nasara
A cewar Gwamnan Katsinan, matakan da gwamnonin yankin Arewa maso Yamma da na jihohin Neja da Nasarawa suka dauka a kan ’yan bindiga suna samun nasara.
“Musamman toshe layin sadarwa na GSM, yanzu masu kiran ’yan bindiga su ba su bayanan mutane ko idan za a kai musu hari, babu yadda za su yi. Sannan babu yadda za a kira mutane ta waya a nemi kudin fansa.
“Hana sayar da mai a yankunan da ke kan iyaka face a gidajen mai da aka kayyade, kuma da rana kadai, sannan babu wanda za a sayar wa na fiye da N5,000, duk sun taimaka.
“Haka ma rufe kasuwannin dabbobi da haramta sayar da kwancen babura a wasu kasuwanni, wanda za mu fadada shi zuwa jihar baki daya domin wadannan mutane da babura suke amfani wajen yin miyagun ayyukan nasu,” inji Masari.
– ’Yan bindiga sun ninka sojoji yawa
Gwamnan ya koka wa ministan cewa ’yan bindigar da ke addabar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya sun ninka yawan jami’an tsaron yankin.
Ya kuma yi zargin cewa duk haka, sojoji na kin hada kai da ’yan banga da ke taimakawa a yaki da ’yan bindiga, alhali gwamnonin jihohin yankin na shirin daukar ’yan banga kimanin 3,000.
“Idan aka horas da ’yan banga 3,000 ’yan sanda za su taimaka wajen samar musu da makamai.
“Amma rahoton da nake samu a Katsina shi ne ’yan banga ba sa samun goyon bayan da ya kamata.”
“Saninmu ne ’yan bindiga sun ninka jami’an tsaro yawa.”
“Su sojoji kuma, ga wadannan jami’an tsaron sa-kai da suka sadaukar da kansu, kuma ku ne kuka ba su horo, suna son su shiga, amma abin da sojojin ke nunawa ya sanyaya mana gwiwa.
“Za mu dauki karin mutum 500, Majalisar Sarakuna kuma za ta dauki 250, amma ta yaya za a samu nasara idan har ba su samu dama yin aiki kafa-da-kafa da sojoji ba?”