✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A binciki mutuwar Janar Attahiru — Dalibai

A kafa wata hukuma mai zaman kanta domin binciken hadarin jirgin saman.

Kungiyar Dalibai Masu Rajin Ci gaba, PSM, ta yi kirna da lallai a gudanar da bincike kan musabbabin hadarin jirgin sama na ranar Juma’ah da ya yi sanadin Hafsan Sojin Kasa Laftanal Janal Ibrahim Attahiru da wasu sojojin.

Shugaban Kungiyar, Mista Bestman Okereafor, ya gabatar da bukatar hakan cikin wata sanarwa a Enugu ranar Lahadi.

“Muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa wata hukuma mai zaman kanta domin binciken yadda hadarin jirgin saman da ya rutsa da Babban Hafsan Sojin Kasa da ma wasu jamián sojan,’’ inji Okereafor.

Ya jajantawa Shugaban Kasa da ma Rundunar Sojan Kasan Najeriya game da faruwar lamarin.

Sannan ya mika sakon ta’aziyyar kungiyar ga sauran jami’an sojan 10 da suka mutu da suka hada da manyan hafsoshin sojan kasa da sauran matsakaita da kananan jami’an sojan kasan da na sama.

A cewarsa, mambobin kungiyar wacce take ’yar kishin Afirka ce – sun samu kansu cikin matukar kaduwa tun bayan faruwar lamarin.

“Ko shakka babu, wannan mummunan koma baya ne a yaki da tsageru da ma ’yan bindiga a kasar nan.

“A bayyane take cewa, a dan karamin lokacin da marigayin Babban Hafsan Sojan Kasan ya yi a kan mukamin ya nuna himma matuka gaya wajen yaki da tsageru a gogewarsa ta fuskar yaki,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN.

Okereafor ya ce kungiyar PSM ta damu matuka kan yawaitar haduran jiragen saman soji a Najeriya duk kuwa da magudan kudaden da ake warewa sojojin a kasafin kudin shekarun baya bayan nan.