✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A bar nada mutanen da ba su da ilimin addini jagororin alhazai – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce bai kamata a rika nada…

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce bai kamata a rika nada mutanen da ba su da ilimin addinin Musulunci a matsayin jagororin alhazai a Najeriya ba.

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da nasiha a Masallacin Juma’a na ’Yan taya da ke Jos, inda ya ce matsayin aikin Hajji a addinin Musulunci da yadda al’ummar Najeriya suka amince da gaskiyar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ba daidai ba ne a rika daukar wadanda ba su da ilimin addinin a matsayin jami’an hukumomin alhazai a jihohin kasar nan.

Ya ce rashin daukar masu ilimin addinin Musulunci a hukumomin alhazan kasar nan ne ke kawo matsalolin da alhazai suke funkanta a kan yadda za su gudanar da aikin Hajji.

 “Babu shakka idan ana daukar masu ilimin addinin Musulunci, za su rika karantar da alhazai yadda za su yi aikin Hajji tun daga nan gida har zuwa Kasa Mai tsarki. Don haka muna kira ga gwamnatocin kasar nan su duba wannan al’amari,” inji shi.

Ya yi kira ga malaman kasar nan su fito su yi magana kan wannan matsala ta rashin daukar masana addinin Musulunci a matsayin jagorin alhazan kasar nan.