Tsohon mai buga wa kasar Ingila kwallon kafa, John Fashanu, ya shiga Jihar Kano domin zabar hazikan ‘yan kwallo 13 da zai dau nauyin ganin sun kware don su mayar da ita sana’a a kasashen Turai.
Ya bayyana wa Aminiya cewar, ta wannan kudirin nasa mai taken “Nemo dan wasa, ka sauya masa rayuwa” (Find a player, change a life initiative) zai hada kai da gwamnatin jiha domin zakulo hazikan ‘yan wasan daga kananan hukumomi 44 na fadin jihar.
Ya ce kuma za su sanya Dillalan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) guda shidda cikin harkar domin tabbatar da an bi cikakkun ka’idojin da suka kamata.
Ya ce kano tana da matasa wadanda suke da fasaha, abinda kadai suke jira shi ne a taimake su domin su zama kwararru.
“Kudiri na shi ne na hada kai da gwamnati kano wajen daukaka kananan ’yan wasa su shiga fagen kwararrun ’yan wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai.
“Bisa sadaukar wa da kauna da nake yi wa Kano, zan dauki nauyin ‘yan wasa 13 daga jihar domin sama musa wuraren sana’ar kwallon a Nahiyar Turai,” inji shi.
A na shi jawabin, Mataimakin Gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce a shirye gwamnati kano ta ke na ganin ta yi kawance kungiyoyi da mutane da suke da niyar taakon matasa ta fannin wasanni.