Wasu kungiyoyin Arewa uku sun bayyana cewa rashin goyon bayan mika mulki ga Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ya fito daga kudancin kasar nan, na iya jefa yankin Arewa cikin rarrabuwar kai musamman a sha’anin harkokin siyasa.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da hadin gwiwar kungiyoyin suka fitar a ranar Laraba, wadda ta ce mika mulki ko goyon bayan Osinbajo a Zaben 2023 shi ne abin da ya dace ga ‘yan arewacin Najeriya.
- Abin da ya sa kawalci wa ’yan bindiga ke neman zama sana’a
- Najeriya A Yau: Me Sabon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Tattalin Arziki Zai Tsinana Wa Talaka?
Sanarwar wadda ta samu sanya hannun Injiniya Daniel Shawulu daga Arewa Consensus Assembly, Suleman Makama daga kungiyar yakin neman zabe na kasa da Khalif Mohammed, sun ce Osinbajo ne zai iya daidaita Najeriya saboda akida ta rashin nuna bangaranci da yake da ita
A cewarsu, yana da tasiri da gogewar da zai iya hada kan ‘yan Najeriya tare da kawar da akidu na banbancin ra’ayi da bangarancin da ake fama da su a kasar nan.
Kazalika, sun bayyana cewa ba da tikitin takara ga wani da ya fito daga kudu kuma mabiyin addinin kirista sannan a hada shi da wani musulmi da zai zame masa mataimaki, shi ne masalaha.
Kungiyoyin sun yi watsi da rade-radin da ake cewar ‘yan Arewa sun kudiri niyyar ci gaba da rike madafun iko ko ganin sun sake darewa kan kujerar shugaban kasa, wanda hakan ke ci gaba da kawo rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan.