Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke da fitattun ’yan takarar Gwamnan a zaben shekarar 2023 da ke tafe. Sai dai sabanin wasu jihohin, a Jihar Kano, akwai ’yan takara da dama da ake jin duriyarsu, kuma ake jin za su taka rawar a-zo-a-gani a zaben.
Sai dai masana siyasa sun fi hasashen takarar za ta fi zafi ne a tsakanin Jam’iyyar APC mai mulki da Jam’iyyar NNPP.
- An ceto mutanen da ’yan bindiga suka sace a gona a Katsina
- Ojukwu da rawar da ya taka a juyin mulkin 1966 (II)
Aminiya ta yi nazari tare da zakulo bakwai daga cikin manyan ’yan takarar Gwamnan Jihar, tare da duba kalubale da damar da kowanensu yake da ita a zaben mai zuwa.
Sheikh Ibrahim Khalil (ADC)
Wannan ba shi ne karo na farko da Sheikh Ibrahim Khalil ke tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano ba, amma wannan ne karon farko da sunansa zai fita a takardar kada kuri’a.
A shekarar 2011 da 2015 ya nemi tsayawa takarar a jam’iyyun ANPP da APC, amma bai kai labari ba aka fitar da shi a zaben fid-da-gwani.
Malamin, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano na da farin jini sosai a tsakanin al’ummar jihar, amma wasu na kallon jam’iyyar da ya fito takara a cikinta ta ADC za ta iya dakushe kaifin tasirin da zai iya yi, musamman idan aka yi la’akari da cewa har yanzu mutanen jihar sun fi mayar da hankali wajen zaben jam’iyya ce, ba dan takara ba.
Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharada (ADP)
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Birnin Kano da Kewaye, Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharada shi ne yake yi wa Jam’iyyar ADP takara. Ya samu takarar ce bayan ya yi rashin nasara a zaben fid-da gwani a tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Kodayake jam’iyyar da ya dauko ana yi mata kallon sabuwa, amma wasu na kallon yadda ya kulla kwance da fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu (Rarara), da kuma farin jininsa musamman a tsakanin matasa, zai iya sa ya taka muhimmiyar rawa a zaben.
Babban kalubalen da zai iya fuskanta shi ne ba ya da dakarun da za su taimaka masa wajen tallata manufofinsa a lungu da sakon jihar, musamman idan aka kwatanta shi da sauran manyan jam’iyyu.
Malam Nasiru Yusuf Gawuna (APC)
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna shi ne dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC.
Mutane da dama na yi masa kallon mai shiru-shiru, wanda bai taba sa-in-sa da kowane daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar biyu na baya-bayan nan ba (Kwankwaso da Shekarau), da kuma Gwamna Ganduje.
Wasu na ganin karfin gwamnati da wancan kallon da jama’a ke yi masa na mai shiru-shiru, kuma mara son hayaniya, na iya taimaka masa matuka.
Sai dai babban abin da wasu ke kallo a matsayin abin da zai iya zame masa tarnaki shi ne yadda jam’iyyun adawa ke tuna wa jama’a a koyaushe cewa shi da Mataimakinsa a takarar, Alhaji Murtala Sule Garo ne, suka yaga sakamakon zaben Gwamna na Mazabar Gama mai cike da ce-ceku-ce a 2019.
Alhaji Bashir Ishak Bashir (LP)
A zaben shekarar 2019, Alhaji Bashir Ishak Bashir ne ya tsaya wa Jam’iyyar PDM takarar Gwamna wannan karon kuma shi ne yake yi wa Jam’iyyar LP takarar.
Kodayake mutane da dama a jihar ba su san shi ba sosai, musamman idan aka kwatanta shi da ragowar ’yan takarar, amma ana ganin tasirinsa zai iya dara na 2019, ko ba komai saboda ana hasashen galibin wadanda za su zabi dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyarsa (Peter Obi), za su iya zabarsa a Kano.
Alhaji Abba Kabir Yusuf (NNPP)
Duk da ana yi mata kallon sabuwar jam’iyya a Jihar Kano, amma alkaluma na nuna cewa yanzu ANPP ita ce babbar jam’iyyar adawa a Jihar Kano, la’akari da tasirin jagoranta na kasa, kuma dan takarar Shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dan jihar.
Ko a zaben 2019, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya zo na biyu a zaben da sai da aka je zagaye na biyu a tsakaninsa da Gwamna Ganduje, kuma a yanzu wasu na kallon fafatawar za ta fi zafi ne a tsakanin Abban da Gawuna na APC.
Babban abin da dan takarar yake tunkaho da shi shi ne farin jini da tarin magoya bayan da Kwankwasiyya ke da shi a jihar.
Alhaji Mohammed Sadik Wali (PDP)
Dan tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali, Alhaji Mohammed Sadik Wali shi ne yake yi wa Jam’iyyar PDP takarar Gwamnan Kano a zaben 2023.
Ana kallon PDP a matsayin daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa a Kano, kodayake karfinta ya yi matukar raguwa bayan ficewar Sanata Kwankwaso da jama’arsa daga jam’iyyar zuwa NNPP.
Babban kalubalen da Sadik ke fuskanta shi ne rikicin cikin gidan da jam’iyyar take fama da shi, musamman kasancewar har yanzu yana kotu da Mohammed Sani Abacha, dan marigayi Shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, wanda yake ikirarin lashe zaben fid-da-gwani na jam’iyyar da aka gudanar.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai (PRP)
Kafin ficewarsa daga Jam’iyyar APC, Alhaji Salihu Tanko Yakasai, hadimi ne kan harkokin yada labarai ga Gwamna Ganduje.
Sai dai yawan sukar lamirin wasu manufofin gwamnatin ya sa aka sauke shi daga mukamin nasa, daga bisani ya bar APC ya koma PRP, inda ya zama dan takarar Gwamnanta.
Ana ganin jam’iyyarsa ta PRP za ta yi tasiri a zaben na 2023, duk da ita ma kamar ragowar takwarorinta, tana da nata tarin matsalolin, musamman rashin wasu kusoshin da za su dafa mata a matakan mazabu da kananan hukumomi.