✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: ‘Tinubu ya zabi Mataimakin takararsa’

“Akwai yiwuwar Ya kasance tsohon Gwamna daga Arewa maso Gabas ”

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya yanke shawarar zaben wanda zai yi masa Mataimaki.

Wata kwakkwarar majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ce ta tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja.

Majiyar ta ce ana sa ran a cikin makon nan dan takarar zai bayyana sunan mutumin a hukumance.

“Akwai yiwuwar wanda aka tsayar takarar Mataimakin ya kasance tsohon Gwamna ne, kuma Sanata mai ci daga yankin Arewa maso Gabas.

“Mutumin Musulmi ne, kamar yadda Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fada ranar Asabar, inda ya ce dan takarar Musulmi ya zaba a matsayin Mataimakinsa,” inji majiyar.

Kazalika, majiyar ta ce Tinubu sam bai yi la’akari da addini ba wajen zabar Mataimakin, sai dai kwarewa da cancanta.

“Babban abin da ya zame wa Tinubu fitila wajen zabin shi ne mutum mai kwarewa wanda zai taimaka masa ya kai Najeriya ga tudun mun-tsira.”

Tun da farko dai Tinubu ya zabi Alhaji Kabiru Ibrahim Masari a matsayin dan takarar Mataimakin nasa na wucin-gadi, gabanin cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tanada.

A ranar Lahadin nan ce ake sa ran dan takarar zai kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ziyarar gaisuwar Sallah a garin Daura da ke Jihar Katsina. (NAN)