Jam’iyyar PDP ta jingine tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyin siyasar Najeirya wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Sakataren Yada Labaran PDP na Kasa, Debo Ologunagba, ya sanar da haka, gami da cewa Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar (NEC) ya nada tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ya jagoranci zaben fitar da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.
- NAJERIYA A YAU: Hatsarin Da Yajin Aikin ASUU Zai Jefa Najeriya
- Ana kama matukan jirgi da mataimakansu 40 sun sha giya kafin tashi sama
Debo Ologunagba, ya ce, “Bayan zuzzurfan tattaunawa, NEC sun yi ittifaki da shawarar Kwamitin Karba-karba na Jam’iyyar PDP na Kasa cewa a bar duk mai sha’awar kujerar shugaban kasa daga kowane yanki ya nema.
“Sannan idan za ta yiwu, jam’iyyar ta yi kokarin ganin an yi sulhu wajen tsayar da dan takara.
“NEC ta ce an yi haka ne domin yin adalci ga kowa; jam’iyyar ta yanke wannan shawara game da karba-karba ne da wuri don kawar da rudani a zaben fitar da dan takara.”
Kakakin PDP na Kasa, Debo Ologunagba, wanda ya sanar da hakan bayan taron NEC da ya gudana ranar Laraba a Abuja, ya Kwamitin Kwamitin Tsare-tsaren Babban Taronta da Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa zai gudanar da taron ne a ranar 28 zuwa 29 ga watan Mayun da muke ciki.
“NEC ta amince a gadanar da babban taro da zaben fitar da tan takarar shugaban kasa a ranar 28 zuwa 29 gawatan Mayu a Abuja
“Sun kuma amince da nadin Sanata David Mark ya jagoranci taron da kuma Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi a matsayin Mataimakinsa, sai tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema a matsayin Sakataren Taron.
“NEC sun bayar da tabbacin yin adalci da kuma gudanar da taron cikin inganci da gaskiya doin a samu ’yan takara da za su fafata a zaben 2023.”
Tun da farko a jawabinsa, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce PDP na da kwarin gwiwa cewa mulki zai dawo hannunta a 2023.
Don haka ya yi kira ga ’yan jam’iyyar d a su sasanta a tsakaninsu domin samun ruwan kuri’u tun daga gundumominsu.