Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce jam’iyyar PDP ce kadai amsar matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu.
Tambuwal ya bayyana haka ne a garin Goronyo da ke jihar a ranar Asabar yayin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda uku a tawagar abokin takarar Atiku
- A kama duk mutumin da ya ki karbar tsofaffin kudi —Gwamnan Zamfara
“Sakon Atiku ga mutanen Goronyo shi ne zai magance musu matsalar tsaro sannan zai bunkasa Dam din Goronya tare da samar da ayyukan yi da tallafa wa matasa don samun ayyukan yi.”
Gwamnan wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Manir Dan Iya, ya ce PDP ta mayar da hankalinta kan matsalolin da talakawan Najeriya ke fuskanta a yanzu.
“Muna da kwarin guiwar fada wa ’yan Najeriya su wane ne mu, kuma me muka shirya yi, muna da tabbacin ’yan Najeriya za su yi alkalanci a lokacin zabe,” in ji Tambuwal.
Gwamnan ya gode wa jama’ar jihar kan yadda suke bai wa PDP da gwamnatinsa goyon baya, sannan ya bukace su da su tabbatar da sun zabi jam’iyyar a zaben da ke tafe nan da mako biyu.