✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Magoya baya a Kano sun ba Jonathan kwana 7 ya fito takara

Matasan sun kuma ce ba su damu da jam’iyyar da zai tsaya ba

Wasu matasa a Jihar Kano sun bai wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan wa’adin kwana bakwai ya  bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023.

Daruruwan  matasan sun yi dafifi a sakatariyar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano a ranar Asabar, bayan da suka gudanar da wani gangami a kewayen wasu muhimman wurare a birnin.

Sun yi amfani da tutoci da fastoci da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban da ke nuna goyon bayansu ga tsohon shugaban.

Wasu daga cikin tutocin da kwalayen suna da rubuce-rubuce kamar su “Jonathan Kar Ka Yashe Mu”, “Kazo Domin Ceto Kasarmu”, “Jonathan, Dole ne ka Tsaya takara”, da dai sauransu.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu Gwamnonin Arewa guda biyu ne ke zawarcin Jonathan a karo na biyu, kuma yana gab da bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar.

Da yake jawabi a sakatariyar ta NUJ,  Shugaban Kungiyar Goyon bayan  Jonathan, Mubashir Tafida, ya ce Najeriya na cikin bakin ciki kuma mutum irin Jonathan ne kadai zai iya gyara matsalolin.

Tafida ya kara da cewa, idan har tsohon Shugaban Kasar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, to matasa miliyan biyu za su mamaye ofishinsa tare da tilasta masa tsayawar.

Ya ce, “Tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya na yin ta’adi. Wannan yana bukatar a gyara, kuma mutum irin Jonathan zai iya yin hakan.”

“Lokacin da yake Shugaban Kasa, babu yunwa da talauci. Makomarmu tana hannunsa. Ubanmu ne, kuma a matsayinmu na yara muna rokonsa da ya tsaya takara domin ya ceto mu daga halin kuncin da Najeriya ke ciki.

“Don haka, mun ba shi wa’adin kwana bakwai ya bayyana sha’awarsa na takarar Shugaban Kasa ko kuma mu yi wa ofishinsa zobe da matasa miliyan 2 don tilasta masa ya bayyana. Makomarmu ta ta’allaka ne a kan sha’awarsa ta tsayawa takara,” inji shi.

Shugaban Kungiyar ya kuma ce ba su damu da wacce jam’iyyar siyasa Jonathan zai tsaya takarar Shugaban Kasar ba.