✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Lalong ya gabatar da kasafin N139bn

Lalong ya ce yana da yakinin kasafin zai biya bukatun al’ummar jihar a badi.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar daftarin Naira biliyan 139 a matsayin kasafin kudin jihar na badi.

Da yake jawabi yayin gabatar da kasafin a ranar Juma’a, Lalong ya ce yana da yakinin kasafin zai biya bukatun al’ummar jihar a badi.

Ya ce idan aka kwatanta da na 2022, kasafin 2023 ya dara da Naira biliyan 32.6.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito Gwamnan na cewa, “Bayan la’akari da halin da al’ummar jihar ke ciki, gwamnati na sa ran kashe Naira biliyan 77.6 kwatankwacin kashi 55.72 na kasafin baki dayansa wajen aiwatar da ayyukan yau da kullum.

“Sannan Naira biliyan 61.7 kwatankwacin kashi 44.2 wajen kula da manyan ayyuka.

“An ware Naira biliyan 13.2 don kula da bangaren gudanarwa, Naira biliyan 31.9 ga bangaren tattalin arziki, sannan Naira biliyan 2.2 ga bangaren shari’a,” in ji shi.

Wannan shi ne kasafi na karshe da Lalong zai gabatar a matsayin Gwamnan Filato, inda ya yi amfani da wannan dama wajen nuna godiyarsa ga Majalisar Jihar bisa goyon baya da hadin kan da take ba shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Majalisar, Yakubu Sanda, ya bai wa gwamnan tabbacin ba za su yi jinkiri wajen amincewa da kasafin ba don amfanin al’ummar Jihar Filato.

(NAN)