Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su karbi kudi daga hannun abokan hamayyarsa idan suka ba su, amma su zabe shi a ranar zabe.
Obi ya yi wannan kira ne a wajen gangamin yakin neman zaben da a aka gudanar a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a ranar Litinin.
- EFCC ta kama Manajan banki kan boye sabbin kudi na miliyan 29
- Kotu ta hana Buhari da CBN kara wa’adin karbar tsoffin takardun kudi
Ya ce, “Ku karbi kudin da za su ba ku saboda dama naku ne, sannan ku zabe ni.
“Muna da sihirin da za mu juya alkiblar Najeriya. Muna da bukatar shugabanci don hade kan Najeriya, wannan shi ne alkawarinmu na farko.
“Mayar da Najeriya sabuwa abu ne mai yiwuwa a karkashin Jam’iyyar LP, ba mu bukatar Najeriya irin wadda macizai da akuyoyi ke hadiye kudi.
“A zaben bana, za su zo muku da batun addini da kabilanci da kuma kudi, amma ku fada musu kuna jin yunwa.
“Za mu iya gina Najeriya irin wadda kowa zai ji dadi. Sama da hekaru 16 suna kamfe da lema da tsintsiya amma babu abin da suka tsinana in ba da rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.
“Yanzu lokacin matsa ne, ku zabe mu don cigaban kasa da kyautata rayuwar al’umma,” in ji Obi.
Tun da fari, Obi da tawagarsa sun kai ziyarar ban girma ga Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, a fadarsa.