A matsayin bangare na shiryen-shiryen zaben 2023, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta fara raba katunan zabe ga wadanda ta yi wa rajista a fadin kasa daga ranar Litinin.
Babban Kwamishinan INEC kuma Shugaban Sashen Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na hukumar, Festus Okoye ne ya sanar da hakan.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi
- Borno Haram Ta Kwace Yankunan Borno ta Arewa —Shugaban Majalisa
A cewar Okoye, an cimma matsayar a fara raba Katin Zaben a wannan Litinin din ne bayan ganawa da kwamishinonin INEC a jihohi 36 da ake da su, hadi da Birinin Tarayya, Abuja.
“Idan ba a manta ba, hukumar ta shirya taron kara wa juna ilimi tare da kwamishinoninta na jihohi a Legas daga Nuwamba, 28 zuwa 2 ga Disamba, 2022.
“A wajen taron ne INEC ta cimma matsaya dangane da tsare-tsaren yadda shirin raba Katin Zaben zai gudana.
“Kazalika, hukumar ta ayyana Litinin, 12 ga Disamba, 2022 zuwa Lahadi, 22 ga Janairu, 2023 a matsayin wa’adin da za a raba Katin Zabe a ofishin hukumar a kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin kasa,” in ji
Aminiya ta tattaro wasu muhimman abubuwa da ya kamata a sani game da shirin raba Katin Zaben na INEC:
- Za a bude cibiyoyin raba katin daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana kullum, har da Asabar da Lahadi.
- Za a raba katin ne a Cibiyoyin Rajista/Gundumomi 8,809 da ake da su a fadin kasa.
- Za a ci gaba da raba katin har zuwa 15 ga Janairu, 2023.
- Bayan 15 ga Janairu, 2023, shirin raba katin zai koma ofisoshin INEC na kananan hukumomi har zuwa 22 ga Janairu, 2023.
- Sai an mika Katin Zabe na Wucin Gadi da aka ba mutum a lokacin rajista kafin a karbi na din-din-din.