✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: ‘Hausawan Ebonyi’ sun goyi bayan dan takarar Gwamnan PDP

Sun kuma ce gwamnatin APC mai ci ta yi watsi da su

Al’ummar Hausawan Jihar Ebonyi sun kai ziyara tare da nuna goyon bayansu ga dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar, Dokta Ifeanyi Odili, inda suka yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin ya samu nasara a zaben da ke tafe.  

Hausawan sun ayyana hakan ne yayin wata ziyara da suka kai wa dan takarar a Abakaliki, babban birnin Jihar ranar Alhamis.

A cewar Shugaban tawagar, Alhaji Idris Datti, dan takarar jam’iyyar PDP ne kadai ke da manufar tafiya da kowa a yakin neman zabensa, inda ya ce gwamnatin Dave Umahi ta yi watsi da al’ummar Hausawa tare da wulakanta su.

Ya ce Hausawa a Ebonyi sun fuskanci wahalhalu a karkashin gwamnatin Umahi wanda ya rika mayar da su saniyar ware tare da hakonsu da sunan yaki da abokan hamayyar siyasa.

A cewar Datti, al’ummar Hausawa ba su taba samun shiga tasku a hannun gwamnatin jihar ba makamancin haka ba, yana mai jaddada cewa Hausawan jihar Ebonyi ba su da wani wurin da za su kira gida illa ita jihar.

Ya tuna cewa gwamnatin tsohon Gwamna, Dokta Sam Egwu ta rungumi Hausawa har ma ta nada shi mai bai wa Gwamna shawara na musamman, amma ta Umahi ta yi watsi da su gaba daya.

A cewar Datti, “Ko da na je Kano ni da ’ya’yana kullum sai su ce mu koma gida, ina gaya musu Kano ai ita ce gidan, amma sai su kafe cewa su fa Ebonyi kawai suka sani.

“Gidan mahaifina da ke Abakaliki ya haura shekara 100. Watakila ma na fi wasu su iya magana da harshen Ibo, amma duk da haka Gwamna Dave Umahi bai dauke mu a matsayin ’yan kasa ba, sannan ya nuna mana ba a maraba da mu.”

Datti ya kuma yi Allah wadai da ayyukan tsagerun kungiyar Ebubeagu, inda ya ce ’yan ta’addan suna farmaki kan al’ummar Hausawa kawai saboda su shafe kabilar.

Ya kara da cewa, “Kungiyar ’yan bindigar na cin zarafin kowa amma sun fi haikewa mu Hausawa. Sun kai mana hare-hare ba tare da mun ci musu komi ba, suna kuma bata mana sunan kabila. Muna rayuwa cikin fargabar rayukanmu, amma duk da haka gwamna Umahi zai je Arewa ya yi karyar cewa yana kula da mu.  Yakan je Abuja ya yi wa shugabanninmu karya.”

Da yake tsokaci kan yanayin siyasar jihar, Datti ya ce al’ummar Hausawan sun amince da dan takarar Jam’iyyar PDP saboda yadda ya yi alkawarin tafiya tare da su.