Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ce babban abun da jam’iyyar PDP ta sa gaba shi ne kamfe da bin hanyoyin cin zaben kasa na 2023, ba tsarin karba-karba ba.
Wike wanda shi ne Shugabantar Kamfen din PDP a zaben gwamna da za a gudanar ranar 19 ga watan Satumba, a Jihar Edo, ya ce mulkin karba-karba gatar jam’iyya mai mulki ce.
“Lokacin da na nemi takara, mutane sun ki amincewa saboda kabilar da na fito, amma a ka yi muhara cewar mu jam’iyyar adawa ne. Abun da muke bukata shi ne mu ci zabe.
“A matsayinmu na jam’iyyar adawa, da farko za mu dubi hanya mai bullewa, wadda za ta taimaka mana mu ci zabe shi ne ya fi komai muhimmanci.
“Jam’iyya mai mulki za ta iya yin maganar karba-karba, amma ita jam’iyyar adawa tana da nata hanyoyin” inji Wike a hirararsa da gidan talbijin na Channels.
Da aka yi masa tambayar game da cece-kuke kan karba-karba, sai ya ce “Ya danganta, a matsayinmu na jam’iyyar adawa za mu kalli duk wasu hanyoyin da za su kai mu ga nasara.
“Babu ruwanmu da wata jam’iyyar. Samun nasara ita zamu sa ka a gaba. Yadda za mu kwato mulkinmu.
“To, kaga ke nan za mu yi amfani da dubaru iri-iri. Saboda haka ba dubara ba ce a matsayina na dan jam’iyyar adawa in yi gaugawar yanke hukunci.
Sai dai mataimakin sakataren watsa labarai na kasa, Diran Odeyemi, ya gaya wa Aminiya cewar, “PDP jam’iyya ce da ke tafiya kan tsari kuma tana ganin darajar karba-karba.
“Saboda haka idan lokaci ya yi za mu bijiro da tsarin karba-karba wanda zai bayyana daga ina Shugaban Jam’iyya zai fito da kuma a ina dan takarar shugabancin kasa zai bullo”, inji Odeyemi.