Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya yi watsi da ikirarin cewa yana da burin tsayawa takarar kujerar Mataimakin Shugaban Kasa a babban zaben kasa na 2023.
A kwanakin da suka gabata ne Dogara ya yi kaura daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya bayyana sabanin ra’ayin siyasa tsakaninsa da Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad na jam’iyyar PDP, a matsayin dalilinsa na sauyin sheka.
Tun bayan haka ne mabiya kafafen sada zumunta suka rika jita-jitar manufar da ta sanya tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ya sauya sheka zuwa APC bayan wani dan takaitaccen zango da ya shafe a babbar jam’iyyar adawa.
Aminiya ta lura cewa labarai da hotunan Dogara sun karade zaurukan sada zumunta tare da yin manuniya a kan cewa zai kasance abokin takara ga tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ke shirin neman takarar kujerar shugaban kasa.
Sai dai Dogara cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta bakin mai magana da yawunsa, Turaki Hassan, ya ce jita-jitar ta samo asali ne daga ’yan adawa masu neman dauke masa hankali.
Sauyin shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC ta haifar da tababa a tsakanin al’ummar mazabarsa ta Dass da Tafawa Balewa da Bogoro a Jihar Bauchi.
A yayin da aka samu rabuwar kai a tsakanin al’ummar kananan hukumomin uku, wasu na goyon bayan shawarar da Dogara ya yanke tare da yi masa fatan alheri, wasu kuwa suka gami da caccaka ce ta kaure a tsakaninsu da shi.