Tsohon gwaman jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce gwamnoni ba su da hurumin yanke wa jam’iyya hukunci game da tsarin karba-karbar kujerar shugaban kasa.
Kwankwaso ya ce babu yadda za a yi gwamnoni su ce za su zauna a wani wuri a yankin Arewa ko a Kudu, su ce sun yanke yankin da zai tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarsu a zaben 2023.
Ya ce zaben yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa abu ne da ya kamata idan za a yi, jam’iyya ta yi la’akari da kowane irin abu da kuma bangarorinta.
Sai dai ya bayyana cewa abu mafi muhimmacin ga jam’iyya shi ne ta tsayar da mutumin da ya dace da kujerar.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise.
A yayin tattaunawar, an tambayi Kwankwao game da tsayawarsa takarar shugaban kasa a zaben 2023, amma ya ce har yanzu bai yanke shawara ba.