✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Akasarin masu neman Shugabancin Najeriya kamata ya yi a ce suna kurkuku – Obasanjo

Sai dai tsohon Shugaban Kasar bai kama suna ba.

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce akasarin masu neman tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a 2023 kamata ya yi a ce yanzu suna kurkuku a tsare.

Ko da dai bai ambaci sunan wadanda yake nufi ba, amma tsohon Shugaban ya ce da hukumomin yaki da cin hanci da bangaren shari’a na aikinsu yadda ya kamata, da ba a ga irin wadannan mutanen na yawonsu kamar kowa ba.

Obasanjo na wadannan kalaman ne a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun ranar Asabar, yayin taron bikin cikarsa shekara 85 a duniya.

Taron dai ya samu halartar manyan baki kamar tsohon Mataimakinsa, Atiku Abubakar da Shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dokta Ngozi Okonjo-Iweala da kuma Shugaban Bankin Raya Kasashe na Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina da sauransu.

Ya zuwa yanzu dai Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar.

Sai dai a cewar Obasanjo, duk wanda ba shi da gaskiya da rikon amana a kananan abubuwa, a manyan ma ba za a same shi da su ba.

Ya ce, “Yanzu ma kamar kowane lokaci, ’yan siyasa suna ta hankoron canza sheka daga wannan jam’iyyar zuwa waccan, a yunkurinsu na tsayawa takara a mukami mafi girma a Najeriya.

“Na kan karanta kuma inji labarin amincewa da kuma nuna goyon baya ga ’yan takarkarin da ban san nagartarsu ba, suna neman amincewar jam’iyyun da ba zan taba goyon bayansu ba.

“Na yi amanna da zabar mutane bisa nagarta da cancanta. Kuma ni a wajena yanzu, babban kalubalen Najeriya bai wuce ganin ta ci gaba daga zamanta na gamin gambiza don ta zama dunkukalliyar kasa daya ba.

“Kuma wannan aikin na hade kan kasa ya fi karfin wani dan takara ko wata jam’iyya ko ma dukkan jam’iyyu; ya fi karfin kowanne bangare na rayuwar al’umma. Dole sai kowa ya zo an hada karfi da karfe don mu gudu tare, mu tsira tare,” inji Obasanjo.