✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2020: Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood

Kusan tun farkon wannan shekarar, duniya baki daya aka fara shiga rudani biyo bayan bullar annobar Coronavirus da aka fara samu a watan Fabrairu a…

Kusan tun farkon wannan shekarar, duniya baki daya aka fara shiga rudani biyo bayan bullar annobar Coronavirus da aka fara samu a watan Fabrairu a Najeriya.

Tun bullar cutar, komai ya tsaya cak bayan dokar kulle da aka shiga, inda aka dakatar da duk wasu abubuwa da suka jibinci taron mutane, ciki kuwa har da harkokin nishadi.

Masana’antar Kannywood, ta shigo shekarar ce a durkushe kasancewar ta dade tana fama da tabarbarewar tattalin arziki da satar fasaha da sauransu.

Tun lokacin da kasuwancin fim ya fara tabarbarewa, wanda ya tursasa forudusoshi da dama daina shirya fina-finai, wadansu kuma suka ajiye fina-finansu suka ki fitar da su.

Masana’antar ta fara shirye-shiryen farfadowa ta hanyar jan hankalin mutane zuwa kallon fina-finai a sinima da sauransu, sai kulken coronavirus din ta dakatar da komai.

 

Nasarorin da aka samu

Fito da sabbin hanyoyin tallata fina-finai

Kasancewar babbar matsalar da ke neman durkusar da masana’antar bai rasa nasaba da tabarbarewar tattalin arzikin masa’antar da rashin isassun sinimomi da za a rika haska fina-finai da dama, sai masu ruwa da tsaki a masana’antar suka fara nemo hanyoyin neman abincinsu.

Daga cikin hanyoyin da aka bi, akwai mayar da hankali wajen yin fina-finai a masu dogon zango a YouTube da kuma nuna fina-finan a tashar Arewa24.

Daga cikin fina-finan da suka fi daukar hankali a bana, akwai Izzar So, da Labarina da Gidan Badamasi da sauransu.

Yawancin zangon shirin Izzar So yana samun masu kallo sama da miliyan daya a YouTube, sai kuma Labarina da Gidan Badamasi da ake nunawa a Arewa24 da ake ta maganarsu.

Haka nan kuma mawakan masana’antar, sun koma rera wakokinsu, su yi bidiyo su sanya a YouTube, mutane su kalla YouTube ta biya su.

Yanzu haka ana samun wakokin Hausa da mutum sama da miliyan biyu suka kalla a YouTube din.

Samun hadin kai

Bayan rikice-rikice da masana’antar ta yi fama da shi, a bana akwai alamun masana’antar ta kama hanyar dinkewa.

Bangarori da dama da a da ake ganin ba sa ga-maciji, yanzu ana ganin su tare musamman a wajen kallon fina-finai a sinima.

Samun filin gina sinima a Kaduna

A watan Satumba ne Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ba masana’antar Kannywood katafaren fili da ya kai girman murabba’i 8,000 domin gina sinima ta zamani a Kaduna.

Idan aka samu sinima ta zamani a Kaduna, za a rage wa ta Kano nauyi, wanda hakan ba karamin cigaba ba ne ga masana’antar.

Manyan fina-finan da aka yi a shekarar

Duk da cewa dokar kullen ta shafi masana’antar matuka, kuma masana’antar ta tsaya cik na tsawon lokaci, masu shirya fina-finai sun yi fina-finai manya.

Jarumar Kannywood Maryam Yahaya

The Right Choice

A watan Disamban bara ne furodusa Abubakar Bashir Maishadda bayan ya shirya manyan fina-finai irinsu Mariya, Hafeez, Sareena da Hauwa Kulu da Wutar Kara da aka ta maganrsu, sai ya ce a tsimaye shi a bana, inda ya dauki alkawarin shirya fim mafi girma a tarihin masana’antar wajen kashe kudi da jarumai.

Abubakar Bashir Maishadda da Kabiru Jammaje ne suka shirya fim din wanda furodusan ya bayyana cewa an kashe masa zunzurutun kudi Naira miliyan 35, kuma ya kunshi manyan jaruman Kannywood da Nollywood.

Daga cikin jaruman fim din akwai Sani Mu’azu da Segun Arinze da Sola Sobowale da Nancy E. Isime da Enyinna Nwigwe da Ali Nuhu da Abba El-Mustapha da Asabe Madaki da sauransu kuma Ali Nuhu ne Daraktan.

Da Aminiya ta tuntubi Abubakar  Maishadda don jin ta bakinsa a kan  abin da ya sa fim din ya zama daban sai ya ce, “Fim din The Right Choice ya zama daban ne domin shi ne fim na farko da aka dauko jaruman Nollywood da dama, inda aka yi hadaka sosai da su, sannan lura da yanayi da lokacin da aka dauka ana yin fim din da yadda aka tsara shi da ma’aikatan da aka sa da abubuwan da fim din ke tattare da su da kuma yadda aka kawata shi, ya sa ya bambanta da duk wani fim na Kannywdood, tun daga kashe kudi da kawata shi da sauransu.”

Har yanzu masu kallo na jiran kallon fim din.

Ali Nuhu da Adam Zango a gidan siniama a Kano

Jalil

Jalil shi ne fim na farko na Kannywood da aka shira kallonsa a birnin Atlanta da ke Arewacin Amurka.

Kamfanin shirya fina-finan Amurka, Nobles Studio shi ne ya shirya fim din.

An shirya kallonsa ne a watan Fabrairu a Plaza Theatre, 1049 Ponce De Leon da ke Atlanta, GA 30306 Amurka, sai dai biyo bayan bullar coronavirus, Aminiya ba ta tabbatar da ko an samu haska fim din.

Kelly D, Lenka ne ya shirya fim din, sannan Leslie Dapwatda ya ba da umarni.

Akwai jarumai irinsu Yakubu Mohammed da Maryam Booth da sauransu a cikin fim din.

Sauran fina-finan da aka shirya da suka dauki hankali akwai Taurarin Boye na T.Y Shaban, wanda Kamal S. Alkali ya ba da umarni da Dafin So na Abnur Entertainment, wanda Sadi N. Mafia ya ba da umarni da Fati na Abubakar Bashir Maishadda da Bana Bakwai na Ali Nuhu da Sarkin Barayi da Manyan Mata da Mati a Zazzau da sauransu.

Sababbin jarumai da suke tashe

A bangaren jarumai, a kullum ana kara samun jarumai maza da mata a masana’antar, amma a bana akwai wadanda tauraronsa ya haska sosai, duk da cewa wasunsu ba sababbi ba ne, amma a bana suka daga.

Daga cikinsu akwai jaruma Mommee Gombe da A’isha Najamu, wadda aka fi sani da A’isha Izzar So da Maryuda Yusuf da Fatima Kinal da sauransu.

Matsalolin da aka fuskanta

Kasancewar a duk masana’antun shirya fina-fina na duniya ba a raba su da rikice-rikice da gaba da sauransu, ita ma Kannywood hakan take.

Daga cikin manyan matsalolin da masana’antar ta fuskanta akwai:

 

Kullen coronavirus

Daga cikin matsalolin da masana’antar ta fuskanta, akwai rufe ta ruf da aka yi saboda kullen coronavirus, inda da dama daga cikin jaruman suka koma kame-kame da neman wasu hanyoyin abincin. Wasu tun kullen, har yanzu ba a fara jin duriyarsu ba.

Bidiyon Maryam Booth

A watan Fabrailu ne aka samu bidiyon tsiraici na fitacciyar jaruma Maryam Booth, wanda ya jawo maganganu.

An ta kai-komo a kan wadanda suka saki bidiyon da dalilan sakin bidiyon.

Wadansu na ganin cewa makiyan jarumar ce suka saki bidiyon don tozarta ta, yayin da wadansu ke ganin tsohon saurayin jarumar da ake zargi da sakin bidiyon.

Lamarin har ya kai ga zuwa kotu.

 

Shigar Rahama Sadau

A wani lamarin kuma, Rahama Sadau ta sanya wasu hotuna da suka nuna wani bangare na jikinta, inda a kasan hotunan aka samu wani wanda ya ci mutuncin Manzon Allah.

Lamarin ya jawo ’yan Kannywood da kansu sun yi Rahama ca, inda har ta kai wasu na zage-zage.